
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Tarayya ta karyata kalaman Shugaban Amurka, Donald Trump na cewa ana kisan gilla ga al’ummar Kiristoci a Nijeriya da kira na a sanya ta cikin jerin ƙasashen da ake da damuwa akansu.
A wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Waje ta fitar a yau Asabar, Daga Kakakinta Kimiebi Imomotimi Ebienfa, gwamnatin ta ce kalaman Trump ba sa nuni ga ainihin halin da ake ciki a ƙasar.
“Nijeriya tana godiya da damuwar ƙasashen duniya game da kare haƙƙin ɗan-adam da ‘yancin addini, amma wannan ikirari ba shi da tushe. ‘Yan Nijeriya mabiya dukkan addinai suna rayuwa, aiki da kuma ibada tare cikin lumana”, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Ma’aikatar ta ƙara da cewa, gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na cigaba da jajircewa wajen yaƙi da ta’addanci, ƙarfafa zumuncin addinai, da kare rayuka da haƙƙoƙin ‘yan kasa baki ɗaya.
Kazalika, ta ce za ta cigaba da yin aiki tare da gwamnatin Amurka domin inganta fahimtar juna kan harkokin yankin gami da ƙoƙarin da ake yi wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a ƙasar.
