Cardoso da mataimakansa na fuskantar bincike kan zargin karya dokar aiki da almundahana

Spread the love

Shugaban babban bankin Nijeriya na fuskantar tuhuma a kan yadda ya ke sanya hannu a takardu barkatai domin jin daɗin shi da sauran shugabannin bankin.

Shaidu da dama daga bankin sun shaida yadda shugaban da Mataimakan sa huɗu suke ƙokarin azurta kansu da dukiyar ƙasa ta hanyar ba kansu alawus-alawus da ya wuce hankali. Wannan na zuwa a lokacin da a ka kawo Cardoso ya gyara irin ɓarnar da magabacinsa Emefiele ya yi a lokacin ya na gwamnan babban bankin.

Ɗaya daga cikin tuhumar da ake ma shugabannin bankin ya haɗa da sanya hannu a kan ƙarin alawus ɗin gida da ya kai Naira biliyan ɗaya a shekara duba da dukkaninsu suna zaune a cikin gidajen alfarma da ke unguwar Maitama a Abuja.

Ƙari cikin tuhume-tuhumen ya haɗa da bai wa kansu kuɗin tafiya ƙasar waje a tsarin ajin farko ba madaidaici ba. Tikitin jirgi ajin farko daga Nijeriya zuwa birnin New York ya na kaiwa dala 15,000, a wannan yanayin matsin rayuwa da ‘yan Nijeriya ke fama dashi.

Ba a nan zargin ya tsaya ba, a na zargin shugabannin bankin da yarda da ƙarin kuɗin kashewa na tafiya ƙasar waje zuwa dala 7000 duk rana, hakan ya nuna a sati za su iya damu aƙalla dala 50,000 banda sauran alawus da ka iya biyo baya.

An cigaba da zargin gwamnan bankin da ɗaukar hayar ƙwararru wanda albashin su ya haura Naira Miliyan 30 ko wanne wata. Waɗannan ƙwararrun an yi ittifaki cewa basu da gogewa a harkokin kuɗi na duniya, amma suna aiki a matsayin Daraktoci a bankin.

Bayan sallamar ma’aikata da dama daga bankin domin gyara tsarin aikin, sai a ke samun labarin a na ɗaukar wasu ma’aikatan ta bayan fage, kamar yadda muke jin labarin a an ɗauki wani ɗan sanda mai ritaya aiki a matsayin Darakta a bankin, inji wani da yace a sakaya sunansa.

Waɗannan tuhume-tuhumen na zuwa ne a daidai lokacin da ake tunanin shugaban babban bankin Yemi Cardoso zai kawo gyara a tsarin bankin, sai dai shima da alama duk kanwar ja ce.

By ukarofi