
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Gwamnatin Tarayya ta ɗauki matakin inganta harkokin cin gashin-kai na ƙananan hukumomin Najeriya baya da ta naɗa kwamitin mutane goma da su ka ƙunshi ministoci da wasu manyan jami’an gwamnati don kula da ɓangaren.
Kwamitin ƙarƙashin jagorancin sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume, an ɗora masa nauyin tabbatar da hukuncin kotu na ranar 11 ga watan Yuli, 2024 wanda ya bai wa kowace ƙaramar hukuma a baki ɗaya jihohin Najeriya ƴancin cin gashin-kai ya fara aiki tare da kula da gudanarwarsa.
Daraktan hulɗa da jama’a na ofishin sakataren gwamnatin, Segun Imohiosen ya fitar da sanarwar cikin wata takarda a Abuja inda ya ce kwamitin na da muhimmanci wajen tabbatar da zartar da dokar wanda kotun ƙoli ta yi don inganta su da kuma gudanar da harkokinsu ba tare da jagorancin gwamnatocin jihohinsu ba.
Mambobin kwamitin sune; Sanata George Akume a matsayinsa na shugaba, ministan kuɗi, ministan tattali, Antoni Janar na Ƙasa, ministan shari’a, ministan kasafi da kuma Akanta Janar na Ƙasa.
Sauran sun haɗa da; gwamnan babban bankin Najeriya, babban sakataren ma’aikatar kuɗi da kuma shugaban hukumar kula da ayyukan haraji.
Sannan za a samu wakilai daga gwamnatocin jihohi da na ƙananan hukumomi domin tabbatar da kwamitin ya samu taimakon gudanarwa daga matakai da dama don cimma nasara a yayin ayyukansa.
Ta ƙara da cewa, matakin wani ɓangare ne na ƙoƙarin Shugaba Tinubu wajen ganin gwamnatinsata ta tabbatar da mutunta kuɗin tsarin mulkin ƙasa da kuma inganta harkokin gwamnati tun daga tushe.
