Dalilin da ya sa Ajaero ba zai amsa gayyatar ‘yan sanda ba – Falana

Spread the love

Sanannen lauyan nan mai rajin kare hakkin ɗan Adam Femi Falana ya bayyana dalilan da ya da Shugaban ƙungiyar ƙwadago Joe Ajaero ba zai sami halartar gayyatar da hukumar ‘yan sanda tai masa ba a kan zargin ta’addanci da laifukan yanar gizo.

Falana ya bayyana cewa, Ajaero ya na da abubuwan yi a tsare ga dukkan ranakun watan kafin samun gayyatar. A dalilin haka, Ajaero ya rubutawa hukumar ‘yan sanda cewa ba zai samu halartar gayyatar ba sai 29 ga watan Agusta 2024.

Falanan a takardar da ya rubutawa hukumar ya bayyana cewa, suna buƙatar ƙarin haske a kan zargin da ake wa shi Ajaero game da ta’addanci, laifukan yanar gizo da cin amanar ƙasa a matsayin su na lauyoyi masu wakiltar ƙungiyar ƙwadago.

By ukarofi