Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
‘Yan jarida fiye da 40 suka halarci taron ƙara wa juna sani kan inganta samo tare da aikawa da labarai wanda cibiyar raya dimokuraɗiyya ta ƙasashen Afrika ta Yamma ta shirya a Katsina.
‘Yan jaridun da suka halarci horas wa sun haɗa da na kafofin yaɗa labarai na gida Najeriya da ƙasashen waje da gidajen rediyo da talabijin da kuma masu aikawa da labarai ta yanar gizo.
Horan yafi mai da hankali wajan tace da tabbatar da sahihancin labari kafin amfani da shi.
Haka kuma an tabo illar rubuta labarai na bogi da abinda ka biyo baya bayan an buga irin waɗannan labarai.
Da yake bayani kan masu mallakan kafofin yaɗa labarai suke biyan buƙatar kansu, ɗaya daga cikin waɗanda suka shirya horon Ahmad Aluko ya ce babu abinda wani zai yi dangane da wannan lamari.
Ya shaidawa mahalarta taron cewa gwamnatin jihar ko ta ƙasa na kafa gidajen rediyo da talabijin ne domin buƙatar kanta,haka ma mutanen da suka mallaki gidan jaridu ko rediyo da talabijin suma sunyi haka ne domin buƙatar kansu.
“Da yawan su na mallakar kafofin yaɗa labarai yadda suke so ayi haka dan jaridar da kake masu aiki zai yi ko ya san nayi,”Inji Ahmad.
Da yawa mahalarta taron sun nuna gamsuwa da irin darussan da su ka koya wanda a cewar su ya ƙara wasa ƙwaƙwalwar su musamman akan abinda ya shafi tace da tabbatar da sahihancin labari.
Cibiyar ta bada horo kan yadda manema labarai za su inganta labarai da kuma sauran abinda ya shafi sanin labarai na gaskiya da na ƙanzon kurege.
An ɗauki kwanaki biyu ana gudanar da taron horas wa a ɗakin taro na Katsina Guest Inn.
