Ganduje ya janye shirin kafa ‘sabuwar Hisbah’ a Kano

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya dakatar da shirinsa na kafa rundunar Hisbah mai zaman kanta a jihar.

Ganduje ya dakatar da shirin nasa ne bayan ce-ce-ku-ce da hakan ya haifar da kuma haramcin da gwamnatin jihar ta sanya kan lamarin.

A cikin wata sanarwa da jigo a Jam’iyyar APC, Baffa Babba Dan-Agundi, ya fitar a madadin Gandujen, ya ce matakin ya biyo bayan tattaunawa da Gwamnatin Kano, da hukumar tsaro ta DSS, domin tabbatar da zaman lafiya a jihar.

A kwanakin baya, Ganduje, wanda shi ne tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, ya bayyana shirin ɗaukar ma’aikatan Hisbah 12,000 da gwamnatin jihar ta sallama, domin su shiga wata ƙungiyarsa ta Hisbah mai zaman kanta.

Ya ce ƙungiyar za ta yi aiki ne ƙarƙashin gidauniyarsa ta Ganduje Foundation, kuma tuni aka fara raba takardun rijista ga masu sha’awar shiga a matsayin ’yan sa-kai.

Sai dai gwamnatin jihar ta haramta wannan shiri, tare da bayar da umarnin ɗaukar matakan tsaro kan duk wani yunƙuri da ya shafi hakan.

Amma bayan wasu ’yan kwanaki, wani jigo a jam’iyyar APC a Kano kuma Darakta-Janar na Cibiyar ƙasa ta Samar da Aiki, Baffa Babba ɗan-Agundi, ya sanar da sabon matakin a madadin tsohon gwamnan.

ɗan-Agundi, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya ce an ɗauki wannan mataki ne bayan wani taron masu ruwa da tsaki da ya haɗa wakilai daga ƙananan hukumomi 44 na jihar.

Ya ce an gudanar da taron ne a ofishin kamfen ɗin Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ke Kano.

ɗan-Agundi ya bayyana cewa an yanke shawarar janye shirin ne bayan martanin jama’a da damuwar da aka nuna sosai game da shirin kafa wata rundunar Hisbah ta daban.

Ya ƙara da cewa manyan masu ruwa da tsaki sun shiga tsakani a lamarin, ciki har da Gwamnatin Jihar Kano, Hukumar Tsaron Fararen Hula ta ƙasa (DSS), da kuma Ganduje da kansa, da nufin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Kano.

Sanarwar ta kuma jaddada girmamawa ga Hukumar Hisbah ta Jihar Kano da aka kafa bisa doka, tare da nuna ƙudurin goyon bayan hukumomin tsaro na ƙasa wajen tabbatar da doka da oda, da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma a faɗin jihar da ƙasa baki ɗaya.

By ukarofi