‘Rayuwarmu tana cikin haɗari’: Akpabio ya roƙi Tinubu ya sake duba dokar janye wa manyan mutane ƴan sanda

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, ya yi magiya ga Shugaba Bola Tinubu da ya sake duba umarninsa na janye jami’an ƴan sanda daga gadin manyan mutane, yana mai bayyana dalilai na tsaro ga ƴaƴan Majalisar Dokoki.

A ranar 23 ga watan Nuwamba Shugaba Tinubu ya umarci a gaggauta janye jami’an ƴan sandan da aka tura gadin manyan mutane a faɗin Nijeriya da nufin warware matsalolin tsaro da ke cigaba da taɓarɓarewa a ƙasar.

Shugaban Majalisar Dattawan ya yi roƙon ne a madadin ƴan majalisu akan umarnin da Tinubu ya bayar na janye jami’an daga ba wa manyan mutane kariya a gidaje da ofisoshinsu.

Akpabio ya ce, a halin da suke ciki yanzu wasu ƴan majalisa ba za su iya zuwa garuruwansu ba saboda babu ƴan sandan da za su basu kariya daga mahara, lamarin da ya sa suka shiga cikin damuwa da tashin hankali.

Akan haka ne ya roƙi Shugaban Ƙasar da ya sake duba umarnin da ya bayar na janye ƴan sanda daga jikin manyan mutane, domin rayuwarsu na cikin hatsari, kamar yadda ya bayyana.

By Babaji