Borno: Dakarun tsaro sun daƙile harin ƴan ta’adda a tsaunikan Mandara zuwa Bitta

Spread the love

Dakarun rundunar atisayen Haɗin Kai (OPHK) sun yi nasarar daƙile wani yunƙurin kutsawar ƴan ta’adda zuwa garin Bitta da ke Jihar Borno, inda suka kashe da dama daga cikinsu a yayin da suka arrangama.

A wata sanarwa da Kakakin dakarun OPHK, Sani Uba ya fitar a ranar 18 ga watan Disamba, ya ce al’amarin ya faru da misalin ƙarfe 12:30 na dare a ranar a lokacin da dakarun suka gano motsin ƴan ta’addan daga tsaunin Mandara ta hanyar na’urorin sa ido na zamani.

Bayan barin ƴan ta’addan su kusanto har zuwa inda ya dace, dakarun suka buɗe wuta tare da kashe da dama daga cikinsu, ciki har da wani babban jagoran ƴan ta’adda da kuma mai ɗaukar hotonsa.

Yayin da sauran ƴan ta’addan ke ƙoƙarin tserewa, rundunar sojin sama ta OPHK ta kai farmaki ta sama, lamarin da ya jefa babbar damuwa ga masu tserewar tare da tarwatsa hanyoyin tsallakarsu.

Haka kuma, bayan artabun, dakarun sun ƙwato makamai da kayayyaki da dama, ciki har da bindigogi kirar AK-47, harsasai, na’urorin sadarwa, wayoyin hannu, da kuma babura da kekuna.

Rundunar ta ce ƙwarin’gwiwar dakarun na nan daram, kuma za su cigaba da ayyukansu domin hana ƴan ta’adda sake samun sarari, tare da tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Arewa maso Gabashin Nijeriya.

By Babaji