Chadi ta mayar wa Nijeriya sama da mutane 600 na wasu jihohi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnatin Chadi ta mayar wa Nijeriya mutane kimanin 600 da ke ayyukan bara a sassa daban-daban na ƙasar.

Rahotonni sun bayyana cewa, dubunnan ƴan gudun hijira daga Jihar Borno ne suka watsu zuwa ƙasashen Chadi da Kamaru sakamakon yaƙin Boko Haram tun daga shekarar 2019.

Darakta-Janar na Hukumar bada Agajin Gaggawa (SEMA), Muhammed Barkinɗo ya bayyana hakan wa manema labarai a Maiduguri, a lokacin da su ke tantance ƴan gudun hijira inda ya ce ƴan bulaguron, mutane ne daga Jihohin Borno, Kano, Sakkwato da Kaduna waɗanda suka shiga Chadi ba tare da cike ƙa’idodi ba.

Barkinɗo ya ce mafi yawancin su suna rayuwa ne a wulaƙantaccen yanayi inda har ta kai ga sun koma bara a titina wanda da shi suka dogara.

Ya kuma ce SEMA ta tallafa musu da wasu kayayyakin amfani da kuɗin mota N10,000 ga kowannen su don komawa jihohinsu.

Kazalika, ya ce da yawa daga cikinsu sun nuna zaƙuwa ta son koma garuruwansu saboda halin matsi da suka tsinci kawunansu.

By Babaji