Cibiyar CBER ta Ingila ta karrama shugabar NSUK

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Cibiyar nazarin kasuwanci da tattalin arziki (CBER) da ke ƙasar Ingila ta karrama shugabar babban jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi (NSUK), Farfesa Sa’adatu Hassan Liman da wata lambar yabo ta musamman da ake kira “fellowship award” a turance.

Da yake sanar da hakan a cikin wata sanarwa ta musamman ga manema labarai, mataimakin shugaban jami’ar NSUK ɗin a fannin ilimi, Farfesa Ari Maikano ya bayyana cewa CBER cibiyar bincike ce ta kasuwanci da tattalin arziki na duniya baki ɗaya wadda aka kafa a ƙasar Ingila a shekarar 2006 da manufar bunƙasa, karramawa da kuma tallafawa a fannin binciken kasuwanci da tattalin arziki.

A cewar Maikano, kyautar ta tabbatar da kyakkyawan jagorancin shugabar jami’ar NSUK, Farfesa Sa’adatu Hassan Liman da kuma kyakkyawan gudumawar da take bayarwa a fannin kasuwanci da tattalin arzikin jihar, Najeriya da duniya baki ɗaya.

Ya ƙara da cewa an karrama shugabar jami’ar NSUK ɗin ne a wani wajen taro da aka gudanar a Said Business School, Jami’ar Oxford, UK kenan kwanan nan.

Maikano ya kuma nuna cewa taron ROGE-Oxford 2025 wanda CBER ta shirya ya haɗo masu ilimi, ƙwararru, masu tsara manufofi, da masu bincike daga kowanna ɓangaren duniya don tattaunawa kan muhimman batutuwa da suka shafi ci gaban kasuwanci da tattalin arziki.

Ya cigaba da bayyana cewa “karramawar da aka yi wa shugabar mu a wannan taron tattalin arzikin duniya baki ɗaya ya nuna himmatarta ne wajen bunƙasa ilimi da inganta ɗorewa a tattalin arzikin duniya.

“Lalle ne, gabatar da takardarta mai taken “Leadership Diversity, Equity and Inclusion (DEI) in organisational success: Perspectives from Leaders and Followers a turance” ya nuna ƙwarewar ta da jagorancinta a fannin.

“Wannan nasarar ta kuma nuna himmatarta wajen jagorancin jami’a a fannin ilimi mai tsayi, a duniya baki ɗaya. Muma a nan muna taya ki murna wato Farfesa Sa’adatu Hassan Liman kan wannan nasarar da ki ka yi fice,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa kyautar da ta samu ba wai kawai tabbacin ƙwarewar ta ba ne, har ma da nuna himmar jami’ar wajen bunƙasa ilimin zamani, bincike, da kuma karramawa.

“Muna alfahari da shugabar tamu da ta wakilci cibiyar ilimin mu ma akan wannan muhimmin yanayi, kuma muna fatan ta ci gaba da bayar da gudunmawa wajen tsara yanayin tattalin arzikin duniya,” in ji shi.”

By ukarofi