
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Fasinjar Ibom Air da aka tsare bisa zargin farmakin wanda ya yi ƙoƙarin tsayar da ita a filin jiragen sama, ta musanta shigar da ƙarar Naira biliyan 500 akan Gwamnatin Tarayya da Hukumar Kula da Zirga-zirgar Jiragen Sama, NCAA.
Emmanson ta bayyana haka ne ta kafar Instagram, ranar Asabar.
Hakan ya biyo bayan rahoton da ke cewa fasinjar ta wani lauya mai suna Ayodele Ademiluyi, ta shigar da ƙara a wata kotun Legas inda ta nemi a biya ta biliyan N500.
Saidai, Emmanson ta nesanta kanta daga lauyan, inda ta ce kawo yanzu ba ta shigar da ƙara akan gwamnatin ko Ibom Air ba.
Ta kuma ce, idan ma za ta shigar da ƙara akan kowane ɓangare, to za a ji ne kai-tsaye daga gare ta.
Don haka ta ce wannan rahoton ba gaskiya ba ne, abu ne da aka ƙirƙira da nufin ruɗar da al’umma, tana mai jaddada cewa ba ta ɗauki matakin doka ba a halin da ake ciki.
Haka kuma, Emmanson ta bayyana cewa lauyanta shine Adam Atakpa na Kippraise Attorneys, tana mai kira ga ɗaukacin al’umma da su ƙaurace wa rahoton shigar da ƙarar da aka jingina mata.
