PDP ta zargi APC da yin amfani da sojoji wajen hargitsa zaɓen cike gurbi a Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Jam’iyyar PDP mai mulki a Zamfara ta zargi jam’iyyar APC reshen jihar da yin amfani da sojoji a lokacin zaɓen cike gurbin ɗan majalisar dokokin jihar a ƙaramar hukumar Ƙaura Namoda ta kudu.

Shugaban jam’iyyar na jiha Jibo Magayaki Jamilu ne ya bayyana hakan a wata ganawa da manema labarai a ofishin sa a yau Lahadi.

A cewarsa, sojojin sun mamaye ƙauyen Sakajiki inda suka fatattaki masu zaɓe daga rumfunan zaɓe, dalilin da ya sa ba a gudanar da zaɓen a yankin ba.

“Dalilin da ya sa hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ta bayyana zaɓen bai kammalu ba, ba a gudanar da zaɓe a ƙauyen Sakajiki ba, domin jam’iyyar APC reshen jihar ta ɗauki hayar jami’an soji da suka fatattaki masu kada ƙuri’a daga rumfunan zaɓen su a lokacin da ake tsaka da gudanar da zaɓe.”

“Jam’iyyar APC ta ɗauki hayar sojoji waɗanda suka mamaye dukkan rumfunan zaɓe ba don kare rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa ba sai don muzgunawa tare da azabtar da masu zaɓe”. Yace

Jibo ya bayyana abubuwan da APC da sojoji suka yi a matsayin wanda bai kamata ba, ya saɓawa tsarin dimokuraɗiyya da kuma saɓawa kundin tsarin mulkin ƙasa.

Ya ce jam’iyyar ba za ta lamunci faruwar irin wannan abu ba, yana mai kira ga hukumomin da suka dace da su ɗauki matakan da suka dace don ganin an kammala zaɓen cikin kwanciyar hankali a jihar.

By ukarofi