Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Sashen gyaran motoci, watau Central Mechanical Workshop da ke cibiyar KYCV mallakan gwamnatin jihar Katsina ta kammala gyara da sabunta motocin gwamnati guda tara, wanda hakan na nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen kula da kadarorin gwamnati da rage asarar kuɗi.
Shugaban cibiyar, Injiniya Kabir Abdullahi Ƙofar Soro, ya bayyana ga manema labarai ya ce nasarar aikin ta ƙara tabbatar da ƙudurin gwamnatin jihar na inganta amfani da kadarorin gwamnati cikin tsari mai inganci da tanadin kudi.
Injiniya Ƙofar Soro ya bayyana cewa motocin Toyota Hilux guda biyu, an yi musu cikakken gyara da sabuntawa tare da daidaita su.
Ya ce gyaran ya ƙunshi aikin gyaran inji, wayoyin wuta da gyaran jikin motocin, wanda hakan ya tsawaita rayuwar motocin tare da daidaita su da ƙa’idojin tsaro da aiki na zamani.
Haka kuma, kodinetan ya bayyana cewa an mayar da babbar motar Mercedes-Benz 911 zuwa motar aiki tafi da gidanka.
Injiniya Kofar Soro ya jaddada cewa wannan ci gaba na ƙara nuna muhimmiyar rawar da Central Mechanical Workshop ke takawa wajen tallafa wa ayyukan gwamnati ta hanyar ƙwarewar fasaha da ake da ita a cikin gida.
Ya ƙara da cewa wannan mataki zai rage dogaro da kamfanonin waje, tare da tabbatar da amfani da dukiyar jama’a kamar yadda ya kamata.
Matasa da ke samun horo a cibiyar suka gudanar da gyare-gyaren motocin.
