Cigaban Nijeriya na da nasaba da jagorancin Tinubu – Shettima

Spread the love

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na cike da ƙwarin gwiwa da tsare-tsare masu inganci, wannan ya sanya Najeriya ta shiga sabon matakin ci gaba.

Ya ce tsarin shugabancinsa ya haifar da damammaki da za su ja hankalin masu zuba jari daga ciki da wajen ƙasar.

Shettima ya bayyana haka ne a yayin wani taro da ya gudana a fadar shugaban ƙasa tare da ministoci da shugabannin hukumomi, inda ya buƙaci su shirya tsaf domin tattaunawar da za a yi da Brazil.

A cewarsa, ya kamata a samu cikakken shiri da fahimtar batutuwan da za a tattauna a yayin ganawar.

Ministan noma da tsaron abinci, Abubakar Kyari, ya ce wannan tattaunawa za ta zama wata babbar dama wajen bunƙasa harkar noma a Najeriya. Haka zalika, Ministan al’adu da yawon buɗe ido, Hannatu Musawa, ta bayyana cewa akwai ‘yan asalin Najeriya da dama a Brazil da ke sha’awar al’adun Najeriya, tare da fatan inganta haɗin gwiwa a fannin ƙirkire-ƙirkire.

A ɓangaren tsaro kuwa, Ministan tsaro, Muhammad Badaru, ya ce an shirya tsaf domin sanya hannu kan yarjejeniyar tsaro da Brazil, wanda zai taimaka wajen kafa cibiyoyin ƙera makamai a Najeriya.

Haka kuma, Ministan Lafiya, Mohammed Ali Pate, ya ce ana sa ran haɗin gwiwar zai taimaka wajen samar da magunguna da alluran rigakafi a cikin gida, tare da bunƙasa harkokin kiwon lafiya.

By ukarofi