
Daga BELLO A. BABAJI
Majalisar Dokoki ta Majalisar Ɗinkin Duniya (IPU), ta ce za ta yi aiki akan ƙorafin da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta shigar a wajenta kan dakatarwar da Majalisar Dattawan Nijeriya ta yi mata na wata shida da zargin cin zarafi da ta yi akan Shugaban majalisar, Godswill Akpabio.
A lokacin da ta ke magana a taron mata na IPU da aka yi a Birnin New York na Amurka, Natasha ta sanar da IPU batutuwan biyu da suka samo asali daga tsarin zama a zauren Majalisar Dattawan, inda ta bayyana dakatarwar a matsayin abinda aka mata ba bisa doka ba.
An dai dakatar da ita ne akan rashin biyayya da saɓa wa dokokin majalisar, ta na mai neman majalisar a mataki na duniya da ta tsoma baki kan batun don a yi adalci.
A kalamanta game da lamarin, Shugabar IPU, Tulia Ackson ta ce ta karɓi koken Sanatar tare da yi mata alƙawarin bin matakin da doka ta amince da su wajen warware rikicin.
Ta ce, jin ɓangaren Natasha kaɗai ba zai zama dalili na su yanke hukunci ba, inda ta ce lallai sai sun ji ta bakin Akpabio kafin su san mataki na gaba da za su ɗauka akan al’amarin, kamar yadda ta bayyana a yayin zaman a wani faifan bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta.
