Daga AISHA ASAS
Taron shekara-shekara na masu ruwa da tsaki a harkar fina-finai, wato CinemaCon 2026, ya sake zama cibiyar ɗaukar hankali a duniya, bayan da manyan kamfanonin Hollywood suka gabatar da sabbin fina-finai da trailers ɗinsu a karon farko.
Rahotanni daga manyan kafafen labarai sun nuna cewa, taron na bana ya zarce na baya wajen ɗaukar hankali, musamman saboda irin nauyin ayyukan da aka gabatar da kuma yadda suka jawo hankalin jama’a cikin ƙanƙanin lokaci.
ɗaya daga cikin manyan abubuwan da suka fi ɗaukar hankali shi ne sakin sabbin trailers na fina-finai masu zuwa, waɗanda suka bazu a kafafen sada zumunta cikin sauri.
Masu sharhi sun bayyana cewa, wasu daga cikin trailers din sun samu miliyoyin masu kallo cikin awanni yayin da masoya suka karaɗe kafafen sada zumunta da martani da kuma tofa albarkacin bakinsu kan abinda idanuwansu suka hango.
Ana hasashen wasu fina-finai za su karya tarihin kuɗaɗen shiga a fagen fina-finai, wannan na nuna yadda sha’awar kallon fina-finai ke ci gaba da ƙaruwa duk da ƙalubalen da masana’antar ke fuskanta.
A ɓangare guda, manyan kamfanonin shirya fina-finai sun yi amfani da wannan dama wajen nuna ƙarfinsu a kasuwa. Rahotanni sun nuna cewa, kamfanoni na fafatawa wajen jawo hankalin masu kallo ta hanyar gabatar da sabbin dabaru da fasahohi. Sannan kuma sun fi mayar da hankali kan manyan fina-finai da aka kashe wa kuɗaɗe masu yawa, wataƙila hakan na da nasaba da ƙoƙarin ganin sun ɗaga darajarsu sama da ta abokanan sana’arsu.
Masana sun bayyana cewa, wannan gasa na da matuƙar muhimmanci wajen farfaɗo da kasuwar fina-finai ta duniya.
Masu nazari sun yi imanin cewa, irin wannan taro na taka muhimmiyar rawa wajen tsara makomar masana’antar fina-finai.
Daga cikin tasirin da ake sa ran gani akwai; ƙaruwar masu zuwa gidajen sinima, jawo hankalin masu zuba jari, ƙara ingancin fina-finai.
Haka kuma, ana sa ran cewa sabbin fina-finai da aka gabatar za su taka rawa wajen dawo da kasuwar fina-finai kan turba bayan ƙalubalen da ta fuskanta a baya.
Wasu masana sun bayyana cewa, shekarar 2026 za ta iya zama ɗaya daga cikin mafi nasara ga Hollywood, idan aka yi la’akari da irin shirye-shiryen da aka gabatar.
Sun jaddada cewa, ingancin labarai na ƙaruwa, yayin da fasahar shirya fim na samun ci gaba, duk da cewa buƙatun masu kallo na karuwa.
CinemaCon 2026 ta tabbatar da cewa, Hollywood na kan hanyar shiga wani sabon zamani mai cike da gasa, ƙirƙira, da kuma sabbin dabaru.
Sabbin trailers da aka gabatar sun nuna cewa masu kallo za su fuskanci sabbin abubuwa masu ƙayatarwa a nan gaba, yayin da kamfanoni ke fafatawa wajen samar da abin da zai ɗauki hankalin duniya.
