Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kwankwaso ya yi watsi da zargin cewa shugaban ƙasar na fifita wani yanki, yana mai cewa Tinubu shugaba ne na ƙasa baki ɗaya.
Wani jigo a jam’iyyar APC, Dokta Musa Iliyasu Kwankwaso, ya ce duk da suka da ake yi wa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, musamman daga yankin Arewa, shi ɗin ne dai kuma zai samu gagarumar nasara a Zaɓen 2027.
Kwankwaso ya bayyana cewa maganganun da ke yawo a shafukan sada zumunta da wasu kafofin siyasa ba komai ba ne illa farfaganda da aka saba gani gabanin zaɓe, yana mai cewa ba za su yi tasiri a sakamakon zaɓe mai zuwa ba.
A wata sanarwa da ya fitar, ya ce irin waɗannan dabaru an taɓa amfani da su a baya, musamman a lokacin tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, inda aka yi ta amfani da batutuwan rashin tsaro da ƙabilanci domin yaƙar gwamnatinsa.
Ya ƙara da cewa yawancin matsalolin da ke addabar Arewa, musamman rashin tsaro, ba na wannan gwamnati ba ne kaɗai, yana mai cewa an daɗe ana fama da su tun kafin zuwan gwamnatin Tinubu.
Kwankwaso ya ce duk da ƙoƙarin da marigayi Muhammadu Buhari ya yi wajen yaƙi da rashin tsaro, yankin Arewa maso Yamma ya fuskanci munanan matsaloli kamar satar mutane da hare-haren ’yan bindiga a lokacin mulkinsa.
“Ya kamata al’ummar Arewa su waiwaya baya su duba irin halin da yankin ya shiga a wancan lokaci, inda aka riƙa garkuwa da ɗalibai da kai hare-hare kan al’umma,” in ji shi.
Ya jaddada cewa gwamnati na ci gaba da samar da kayan aiki, kuɗaɗe da ƙarfafawa wa jami’an tsaro, yana mai cewa wajibi ne al’umma su mara wa waɗannan ƙoƙari baya maimakon yawaita suka.
A ɓangaren ayyukan more rayuwa, ya ce gwamnatin Tinubu ta ɗora kan ayyukan da aka fara a zamanin Buhari tare da faɗaɗa su, musamman a Arewa, inda ya ambaci layukan dogo, manyan tituna, noma, samar da ruwa da kuma aikin bututun gas na AKK.
Ya kuma ce ana samun ci gaba a ayyukan layin dogo da zai taso daga Kano zuwa Abuja da Maiduguri da sauran yankuna, wanda ya nuna ƙudirin gwamnati wajen bunƙasa Arewa.
Kwankwaso ya yi watsi da zargin cewa shugaban ƙasar na fifita wani yanki, yana mai cewa Tinubu shugaba ne na ƙasa baki ɗaya.
Dangane da siyasar 2027, ya bayyana ƙwarin gwiwa cewa APC za ta ƙara ƙarfafa matsayinta a Kano da ma Arewa baki ɗaya, yana mai nuni da tasirin manyan jiga-jigan jam’iyyar.
Ya kuma yi watsi da yunƙurin wasu jam’iyyun adawa, musamman ADC, inda ya ce ba su da wani tsari da ƙarfin da za su iya ƙalubalantar APC.
Kwankwaso ya buƙaci ’yan Nijeriya da su yi watsi da masu adawa da gwamnatin APC, su kuma mara wa gwamnatin Tinubu baya domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban ƙasa..
