Cinikin wajen Sin ya ƙaru da kashi 9.4 a watanni 6 na farkon bana

Spread the love

Daga CMG HAUSA

Alƙaluman da babbar hukumar kwastam ta ƙasar Sin ta fitar a kwanakin baya sun nuna cewa, daga watan Jarairu zuwa watan Yuni na bana, kayayyakin da ƙasar Sin ta shigi da fici, sun ƙaru da kashi 9.4% kan makamancin lokacin bara.

Kakakin ma’aikatar kasuwancin ƙasar Sin Shu Jueting ta shedawa manema labarai jiya Alhamis cewa, a cikin watanni shida na farkon bana, cinikayyar waje ta Sin, ta magance matsaloli da dama da suka kunno kai cikin gida da kuma waje, tare da nuna karfin bunƙasuwa ba tare da tangarda ba. Ta ce:

“Yawan kudin dake shafar cinikin shige da fice a watan Yuni, ya kai sabon matsayi a kowane wata. Yadda ake fitar da kayayyaki daga yankin Delta na mashigin kogin Yangtze yana farfadowa cikin sauri, wanda ya ƙaru da kashi 9.3% a farkon watanni 6 na bana. Matakin da ya tabbatar da ƙasar Sin ta zauna a kan matsayin ƙasa mafi girma wajen cinikin kayayyaki a duniya. Sannan yawan kuɗin dake shafar fitar da kayayyaki a watan Jarairu zuwa Maris a kasuwar duniya, ya kai kashi 14.1%, daidai da na makamancin shekarar bara.”

Shu Jueting ta ce, a sauran watanni shida na wannan shekara, yayin da ake ci gaba da fuskantar wasu dalilai na rashin tabbas, darashin kwanciyar hankali a kasuwannin gida da na waje, ma’aikatar za ta mayar da hankali wajen tabbatar da samun bunƙasuwa mai inganci ba tare da tangarda ba ga kamfanonin waje da tsarin samarwa da rarraba kayayyaki a wannan fanni, da taimakawa kamfanoni da haɓaka kasuwanni da bullo da sabbin hanyoyin samun bunkasuwa da sauransu.

Fassarawar Amina Xu

By Editor