Daga BELLO A. BABAJI
Kungiyar ‘yan kishin ƙasa ta COPAN ƙarƙashin jagorancin Barista Uchenna Odielli ta yi alla-wadai da yunƙurin da wani ɗan Burtaniya mai suna Andrew Wynne Povich da aka sani da Free Povey ya yi na kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Bayan zurfin bincike da ‘yan sanda suka yi, sun shelanta neman sa ruwa a jallo kan ɗaukar nauyin wasu mutane a Nijeriya don nakasa ƙasar ta hanyar haddasa tashin-tashina, zanga-zanga da makamantansu.
Cikin wata takarda da COPAN ta fitar a ranar Litinin, ta ce duk wani yunƙuri na kifar da zaɓaɓɓiyar gwamnatin da aka kafa daga ‘yan ƙasar waje, abun a yi tir ne da shi.
Ta ce, hakan karya dokar ƙai’dar cin gashin kan ƙasa ne da saɓa wa dokokin demokraɗiyya da na ƙasa-da-ƙasa.
Ta kuma yi kira ga ‘yan ƙasashen waje da ke zaune a Nijeriya su girmama zaɓin demokraɗiyya da takwarorinsu suke akai da kuma ƙaurace wa ayyukan da suka shafi maƙarƙashiya.
Kazalika, ta buƙaci ‘yan Nijeriya su kasance masu lura tare da bai wa gwamnati goyon baya yayin da ta ke ƙoƙarin magance matsalolin matsin rayuwa da ake fama da shi a ƙasar.
