Courtois zai yi jinya mai tsawo a Real Madrid

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Mai tsaron ragar Real Madrid, Thibaut Courtois zai yi jinya mai tsawo a kakar bana, bayan da ya ji rauni a gwiwar ƙafarsa ta hagu.

A ’yan kwanaki masu zuwa likitoci za su yi wa golan tawagar Belgium, mai shekara 31 tiyata, daga baya a fayyace kwanakin jinyar da zai yi.

Courtois, wanda aka zava mai tsaron raga mafi fice a duniya a bikin kyautar Ballon d’Or a bara, ya lashe La Liga biyu tun bayan da ya koma Real a 2018.

Ya buga wa Real wasa 230, wadda za ta kece raini da Athletic Bilbao a wasan farko a kakar bana ta La Liga ranar Asabar.

Courtois ya lashe kofin firimiya biyu a Chelsea, daga nan ya koma Real Madrid a 2018, ya ɗauki La Liga ɗaya a Atletico Madrid a 2014.

Ya kuma ɗauki Champions League a 2022, wanda ya taka rawar gani da Real ta doke Liverpool a Faransa.