
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), ta ce ta gano wata masana’antar da ake haɗa bindigogi a Jihar Kaduna, inda ta kuma ƙwato bindigun da aka haɗa da kayan da ake amfani da su wajen samar da makamai.
Hukumar ta cimma wannan nasara ne a lokacin da jami’anta suka kai wani samame a yankin Sabon Garin Kangin da ke jihar, a inda kuma yi nasarar suka kama mai ita.
Daraktan yaɗa labaran NDLEA, Femi Babafemi ne ya bayyana haka a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Lahadi. A cewarsa, atisayen jami’an ya yi sanadiyyar ƙwato wasu bindigu da aka kammala haɗa su da kayayyakin da ake amfani da su wajen haɗa ƙarin wasu makamai.
Sannan, hakan ya nuna alaƙar da ke tsakanin safarar ƙwayoyi, amfani da kayan maye da wasu miyagun laifuka acikin al’umma. “Wannan ya ƙarfafa wa ainihin hujjar da aka samu cewa akwai alaƙa tsakanin harkokin maye, safarar ƙwayoyi da wasu miyagun laifuka,” inji shi.
