Da Ɗumi-ɗumi: Kotu ta sahale wa Emefiele tafiye-tafiye zuwa sassan Nijeriya

Daga BASHIR ISAH

 Babbar Kotun Tarayya mai zamanta a Abuja ta aminjce da bukatar da tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Godwin Emefiele, ya nema ta yin tafiye-tafiye a wajen Abuja.

Kotun ta sahale wa Emefiele bukatar tasa ne bisa sharadin dole ya zauna a kasa ba tare da ya ketara zuwa waje ba.

Tun farko, belin da Emefiele ya samu ya nuna ba shi damar fita daga birnin Abuja.