Yadda ‘yan ta’adda suka kai hari a sansanin sojoji a Katsina

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Barayin daji fiye da mutum 100 kan babura dauke da muggan makamai sun kai hari a sansanin jami’an tsaro da ya kunshi sojoji da ‘yan sanda, a sansanin dake garin Nahuta a karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina.

Majiyar Manhaja ta bayyana cewar, sojojin sun mayar da martani ta hanyar bude wa ‘yan bindigar wuta amma barayin sun fi su yawa sun kuma shammace su lamarin da ya tilasta jam’in tsaron janye.

Bayan shafe kimanin sa’o’i biyu da rabi bangarorin biyu na dauki ba dadi, barayin sun samu nasarar kone Kayayyakin hansanin jami’an tsaron da kuma motocinsun daga bisani suka kutsa cikin garin Nahuta, inda suka shiga gidaje da shagunan mutane suka saci kayan abinci da dabbobi da dai sauran Kayayyaki.

Wani mazaunin garin ya bayyana cewar, jajircewar da sojojin sukayi a yayin fafatawar da sun samu taimakon jiragen yaki na sama da sun fatattaki barayin.

Mafi yawan mutanen garin sun fice daga gidajensu, duk da majiyarmu ta ce ‘yan bindigar basu kashe kowa ba, sai dai sun tsoratarda mazaunin garin.

Mazauna garin su gudu zuwa garuruwa mafi kusa kamar irin su Batsari don gudun sake dawowar barayin.

Har zuwa hada wannan rahoton kakakin rundunar ‘yan sanda da na soji a jihar ba su ce komai ba dangane da lamarin.

By Editor