Alƙalan gasa na duba abubuwa da dama wajen ingancin labari – Sulaiman Ibrahim 

“Ka na ƙara karatu hikimarka na ƙara faɗi kan rubutu”

Daga IBRAHIM HAMISU, Kano 

Idan a na maganar gogewa da kwarewa a harkar rubutun littafi da kuma aikin jarida, dole a ambaci sunan Sulaiman Ibrahim Katsina, wanda littafin da ya rubuta na ‘Turmin Danya’ ya lashe kyautar littafin da ya fi kowane inganci a Nijeriya a cikin shekaru 41 da ta gabata. A zanyawarsa wakilin Blueprint Manhaja a Kano, Ibrahim Hamisu, mai karatu zai san ko wane ne marubucin littafin ‘Turmin Danya’, tun daga tarihinsa, zuwa gwagwarmayar da aka yi, da kuma nasarorin da ya samu a rubutu da ma aikin Jarida. Ku biyo mu:

MANHAJA: Za mu so ka gabatar mana da kanka ga masu karatunmu?

SULAIMAN IBRAHIM: Sunana Sulaiman Ibrahim. Nakan kara da Katsina.

Ko za ka ba mu takaitaccen tarihinka?

Yau shekara biyu da rabi ke nan da na yi ritaya daga gidan rediyon BBC Landan a matsayin mai gabatarwa. Sannan kafin zuwa BBC ni akanta ne a Katsina Polytechnic. Kafin sannan kuma na tava siyasa. Kana duk kafin haka, na yi aikin gwamnati, a lokacin Katsina tana cikin Jahar Kaduna. An haife ni a Katsina shekaru da yawa da suka wuce. Sannan Allah (SWT) Ya albarkace ni da mata guda da ‘ya’ya.

Yaushe aka fara harkar rubutun littafin Hausa?

Na fara rubutun littafai ne a 1978, ina matashi, lokacin da NNPC (Northern Nigeria Publishing Company), Zariya, Kamfanin wallafa na Arewacin Najeriya, ya gayyaci masu sha’awarar shiga gasar rubuta littafi da su aika masa da labarinsu, to shi ne na rubuta ‘Mallakin Zuciyata’. Allah da ikonsa kuma sai ya yi na daya a gasar.

Daga nan kuma sai ita ma ma’aikatar kula da Al’adun Gargajiya ta Najeriya ta kaddamar da tata gasar. Sai kuma na rubuta ‘Turmin Danya’ na aika. shi ma Allah Ya taimaka ya yi na daya.

Wane littafi ka fara rubutawa?

Kamar yadda na fada a baya, ‘Mallakin Zuciyata’ shi ne littafina na farko. Na biyu ‘Turmin Danya’. Sannan ‘Tura ta Kai Bango’.

Ya zuwa yanzu littafai nawa ka rubuta?

Zuwa yanzu littafai uku na rubuta kamar yadda na bayyana su a baya. Amma karin wasu na tafe in sha Allah.

Littafin ‘Turmin Danya’ yana daya daga cikin littafanka da ake amfani da su a Nigeriya ta yaya rubutan littafin ya samo asali?

Da ma ni mai sha’awar karance-karance ne. Jaridun Hausa da na Ingilishi, mujallu da littafan kissoshi da kuma saura a kan ilimomi daban-daban. Daga nan ne fa na fara jin ina son ni ma wata rana in rubuta littafi. Wata rana kuwa kwatsam, sai wani dan’uwa ya gaya man cewa ya ga talla a jarida, kamfanin buga littafai na NNPC, Zariya ya tallata wata gasa ta rubuta kagaggen labari.

Da yake ina da sha’awar rubutun tun tuni sai na yanke shawarar rubutawa a kan batun da nake fata jama’a za su ji dadin karantawa. Na hau rubutu ba-ji-ba-gani. Ana gobe za a rufe gasar na aika da labarin. Can, bayan watanni, sai ga wasika daga NNPC Zariya cewa na yi zakara, ‘Mallakin Zuciyata’ shi ya yi na daya a gasar, ‘So Aljannar Duniya’ ya zo biyu. na uku kuma, ‘Amadi na Malam Ama’. 

Sunanka ya yi fice a bangaren aikin jarida wato sashin Hausa na BBC Hausa da ke Landan. Ta yaya kake hada rubutun littafi da aikin jarida?

To, a gaskiya galibin ayyukan da na yi a lokacin da nake aikin jarida sun fi ta’allaka ne ga aikin jaridar. Bayan aikin BBC na kuma dinga rubuta wa wata jarida ta Najeriya makala kowane mako, ina amfani da wani suna na aro, abin da Ingilishi ake ce wa ‘pen name’.

Bayan shi kuma ga aikin kula da Kwalejin aikin Jarida ta BBC, Sahen Hausa, inda nake rubuta makaloli a kan aikin ko in fassara abubuwan da wasu manyan masana aikin suka rubuta, wadanda na ga za su amfani abokan aiki. Kana ina rubuta gyararraki ga abubuwan da na ji ba daidai ba a shirye-shiryenmu, ko ire-iren su da aka rubuta ba daidai ba a shafukanmu na yana, ko a kan fassara, da ka’idojin rubutu da na aikin, da alkalumma da sauran su.

Mene ne jigon shi wannan littafin na ‘Turmin Danya’?

A taqaice jigon wannan littafi shi ne kishin kasa. Ka san da wuya kasa ta iya ci gaba idan diyanta ba su kishin ta. Manyan hanyoyin rashin kishin kasar kuwa sun hada da satar dukiyar jama’a, da cin hanci da rashawa, da kin biyan harajin gwamnati ko taimakawa wajen kin biya. Don haka, wannan labari a kan yadda ake karya ka’idoji ne a iyakokin shiga kasa da kayyaki – galibi ta hanyar fasa-kwauri.

Jami’in kan iyaka ya sami kudi, dan sumogal ma ya samu, gwamnati kuma ta tashi a tutar babu. Don haka, ba za ta iya gudanar da ayyukan da talakawa suke sanya ran za ta yi masu ba. A taqaice labarin a kan fasa-kwaurin ne da sauran sharrunkan da ke tattare da shi na cin amana, da cin hanci da rashawa, da kyashin juna da cune. Sai kuma soyayya, da sharholiya da shaye-shaye.

A wacce shekara aka fara buga littafin ‘Turmin Danya’ kuma ya zuwa yanzu ina aka kwana dangane da buga shi?

An fara buga Turmin Danya a shekarar 1982, jim kadan bayan nasara a gasa, wadda ita ce ta ba da karfin gwiwar rubuta shi. Kuma bayan mun je Legas ke nan, bayan an yi bukin ba da kyautuka a gare mu, ni da wanda nasa ya zo na biyu da wanda ya zo na uku. Ita Ma’aikatar Al’adun Gargajiya ta Gwamnatin Tarayya ce ta dauki nauyi sanya Kamfanin Wallafa na Arewacin Najeriya (NNPC, Zaria) ya buga shi, ya kuma yi aikin sayar da shi. Sai dai yanzu, bayan da sake sabunta shi na karve aikin wallafa shi daga kamfanin NNPC Zaria zuwa ga Kamfanin Wallafa na Gidan Dabino da ke Kano.

A shekara 41 da ta gabata littafin ya samu nasarar lashe gasa. Mene ne sirrin nasarar littafin?

Ka san alkalan gasa sukan duba abubuwa da dama wajen nazarin ingancin labari. Tashin farko, mai dubawa zai yi kokarin ganin ko rubutun ma yana karantuwa cikin sauki da ma’ana. Sannan, an yi amfani da nahawu yadda ya dace ko a’a? Akwai kuma amfani da kalmomin da suka dace? An yi labarin yadda zai ja hankalin mai karatu ya ci gaba da karantawa, watakila har zuwa karshe? Kagaggen labari ne ko daga wani wuri aka kwafo shi?

An sanya taurarin da suka dace da matsayinsu a labarin?

Ya kamata kuma labarin ya kasance babu cin zarafin wani mutum ko wasu al’ummomi. Akwai bukatar labarin ya zama yana da wani gacin da ake son ya cim ma, yadda idan ya kai shi za a iya sanin an kai ga nasara ko akasin haka a labarin. Akwai kuma bukatar amfani da kwarewa a dabarar rubutu, yadda zai ci gaba da jan hankalin mai karatu har zuwa karewar labari. Bayan bin galibin qa’idojin da na bayyana, ina ganin gina ‘Turmin Danya’ a kan wata matsala da kasa ke fama da ita da kuma iya yakar ta, sun taka muhimmiyar rawa wajen kai labarin ga nasara.

Wadanne shawarwari za ka bai wa matasan marubuta don ganin sun inganta rubutunsu a wannan zamani?

Galibin marubuta masu sha’awar karatu ne. Hakan yana daya daga cikin hanyoyin kara fahimtar harshen da kake rubutun a ciki da yadda ake sarrafa shi. Ta haka kuma za ka ga irin maganganu ko bayanan da in an yi su suke burge ka. Za ka kuma iya ganin abubuwan da kai kake ganin ba yadda aka fade su ya kamata a faxe sun ba. Da za a rubuta su irin yadda kake tunani da zai fi. Kana kara karatu hikimarka tana kara fadi a kan yadda ya kamata rubutu ya kasance.

Ya kuma kamata ka so harshen da za ka yi amfani da shi. Ka fahimci ka’idojinsa da dokokinsa, salon maganarsa da karin maganarsa, yabo a cikinsa, da ba’a da zaurance. Yawan karatu a cikin harshen zai taimaka wajen sanin karin tarin kalmomi, yadda da wuya ka rasa samun kalmar da ta fi dacewa ka yi amfani da ita a wata jumla. Sannan kuma a yi kokarin rubuta abubuwan da za su amfani jama’a, ba wadanda za su cutar da su ba.

Hausa da sauran harsunan gida suna fuskantar barazana daga wajen ‘yan boko, wadanda ko da yake har yanzu suna iya magana da Hausa, ba su faye ko iya rubutu da Hausa ba. Kowane sai Ingilishi. Ko dai don rashin sabo da rubuta Hausar ko kuma don kokarin burgewa tsakanin abokai, wadanda in ba da Ingilishi ka rubuta masu abu ba, sai su ɗauka don ba ka iya Ingilishin ba ne. Wani kuwa da a ce bai iya Ingilishi ba gara a ce ba ya jin Hausa. Zan maimaita cewa lalle jumlolin da aka bude labari da su su sanya mai karatu kwadayin ci gaba da karantawa don fahimtar halin da aka shiga da kuma son jin yadda za a warware kalubalen da aka ci karo da shi.

Bayan ka kammala rubutun, ka bi ka karanta don ganin ko akwai wasu kura-kuren da suka kamata ka gyara, ko kuma salon maganar da ya kamata ka sauya ko ka kara. Ka dai tace shi sau da dama kafin ka tura gaba don wani kuma ya sake dubawa kafin a wallafa shi, kada sai bayan an wallafa ka zo kana da-na-sani.

Mun gode. 

Ni ma na gode.