Kano ta ware N8bn don gina makarantun firamare na musamman guda uku

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gwamnatin jihar Kano ta ware Naira biliyan 8 domin gina manyan makarantun firamare guda uku a fadin jihar.

A cewar Gwamna Engr. Abba Kabir Yusuf, makarantun za su kasance da cikakkun kayan aikin koyarwa, za kuma a samar da isasshen yanayi ga yaran da suka fito daga iyayen marasa galihu domin samun ingantaccen ilimi duka dai don samun ci gaba a nan gaba.

Gwamnan ya ce za a kafa makarantun ne a kowace mazabar majalisar dattawa da kayayyakin koyo na zamani don samar da ingantaccen ilimi a matakin farko.

Ya kuma ce an ware Naira biliyan 6 domin gyara dukkan makarantun firamare.

Ya kara da cewa gwamnati ta amince da gyara wasu cibiyoyi na musamman guda 26 da tsohon Gwamna Rabiu Kwankwaso ya kirkira kuma an kammala guda 17.

“A daidai lokacin da daliban ke karbar darussa a kasa, za mu ci gaba da ba da kulawa ga samar da kayan aikin koyarwa na yau da kullun zai ba wa yaranmu damar samun ingantaccen yanayin koyo da koyarwa.

“Mun kuma kashe Naira miliyan 500 wajen gina hostel a Jami’ar Aliko Wudil sannan kuma an biya Naira miliyan 150 don sabon sashin kula da muhalli da yanayi na Jami’ar Maitama Sule.

“An biya sama da Naira miliyan 500 na Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar don yin sabbin kwasa-kwasai a Jami’ar Wudil da Yusuf Maitama Sule.

“Masu karatun shari’a na Kano da sauran cibiyoyi sun ci gajiyar biyan sama da Naira miliyan 100 domin yin rijistar sabbin kwasa-kwasansu.

“Kusan kashi 93 cikin 100 na kudin koyarwa na daliban Masters 501 a Indiya da sauran kasashen waje an daidaita su kuma an daidaita alawus din su na watanni hudu don ba su damar fuskantar karatun,” in ji Gwamna Abba Kabir

Gwamnan jihar ya kuma ce gwamnati ta biya Naira miliyan 700 a matsayin kudin rajista ga daliban jihar Kano da ke karatu a Jami’ar Bayero ta Kano, sannan ta biya Naira biliyan 1.5 a matsayin hukumar jarrabawar Afirka ta yamma, WAEC, da hukumar jarrabawa ta kasa, NECO, na kudaden jarrabawar. daliban makarantun sakandire na jiha.