Iftila’in Oyo: Dole a binciko masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba don fuskantar hukunci – Tinubu

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Kasa Bola Tinubu ya ce dole ne a binciko tare da hukunta masu harkar haƙar ma’adinai ta haramtacciyar hanyar da suka yi sanadiyar aukuwar fashewa mai karfi a Ibadan, Jihar Oyo.

MANHAJA ta ruwaito Tinubu ya bayyana haka ne cikin sanarwar da ya fitar ranar Laraba ta hannun kakakinsa, Ajuri Ngelale.

Sanarwar ta ce “Abin damuwa ne ainun jin cewa aukuwar fashewar na da nasaba da ayyukan masu hakar ma’adina ba bisa ka’ida ba.

“Dole a binciko masu hannun cikin wannan halin gangancin da ya haifar da wannan mummunan al’amari don su fuskanci hukunci.”

Shugaban Kasar ya yi amfani da wannan dama wajen taya alhini ga Gwamnatin Oyo da ma al’ummar jihar baki daya kan wannan abin tashin hankalin da ya faru.

Kazalika, ya yi kira ga Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) a kan ta yi aiki tare da Gwamnatin Oyo domin bada agajin gaggawa ga wadanda iftila’in ya shafa.

Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya ce fashewar ta auku ne a sakamakon ayyukan masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba a yankin bayan da suka tara kayan aikinsu da ya kunshi abubuwa masu fashewa a wasu gine-gine a yankin Bodija da ke Ibadan, babban birnin jihar.

Rahotanni mabambanta sun ce, an samu asarar rayuka da dimbin dukiya, sannan wasu da dama sun tagayyara a sakamakon fashewar wadda ta auku a ranar Talata da maraice.