Ni ce mace ta farko da ta riƙe muƙamin shugabar matan Jam’iyyar PDP a Jihar Nasarawa – Hajara Ɗanyaro

“Ina yin shigar mutunci don ‘yan baya su koya”

Daga JOHN D. WADA, a Lafiya

Daya daga cikin mata da suka kafa tarihi a Jihar Nasarawa, jajirtacciyar mace da ta tabbatar wa duniya mata ma za su iya a bangaren siyasa, Hajiya Hajara Danyaro Ibrahim ta samu damar amsar gayyatar da jaridar Manhaja ta yi mata, don tattaunawa da ita a wannan shafi na Mata A Yau.

Mace ce mai kamar maza, da ta iya shanye kalubalen da ke tattare da kutsawa cikin maza don neman abinda suke rike da shi, don haka rayuwarta zata iya zama abin koyi ga mata da ke da sha’awar samun makoma irin tata, wato shiga harkar siyasa tare da zama wata tsiya a cikinta.

Honorabule Hajara Danyaro Ibrahim ita ce mace Daya tilo da aka zaba a kujerar majalisar dokokin Jihar Nasarawa don wakiltar mazabar Nasarawa ta Tsakiya. Cikakkiyar ‘yar siyasa ce wacce kafin wannan zaben ta a matsayin ‘yar majalisar dokokin ta Jihar Nasarawa ta rike mukamai da dama.

Wakilin mu a Jihar ta Nasarawa, John D. Wada, ya samu damar tattuana da ita. Hajiyar ta bayyana muhimman batutuwa da suka hada da rayuwarta zuwa gwagwarmayar siyasa da kuma irin nasarorin da ta samu. Baya ga haka, ta bayyana muhimmancin shiga ta al’ada ga macen Arewa da kuma shawarwari da ta bayar domin ‘yan’uwanta mata.
Ga dai yadda hirar yakasance:

MANHAJA: Mu fara da jin tarihin rayuwarki a takaice.

HAJIYA HAJARA: Sunana Hajiya Hajara Danyaro Ibrahim. An haife ni a garin Nasarawa Hedekwatar Karamar Hukumar Nasarawa anan Jihar Nasarawa. Ina da aure da maigidana mai suna, Alhaji Abubakar Sadik Ubandoma. Muna da ‘ya’ya. Na yi karatun firamari dina a Kofar Kudu anan Nasarawa. Daganan na yi sakandare dina a G.S.S. Nasarawa. Na cigaba a makarantan kimiya da kere-kere na tarayya shima anan Nasarawa inda na samu babban difoloma. Daganan na cigaba a babban jami’ar Jihar Nasarawa inda na samu digiri da kuma master digiri dina. Daganan na yi aikin banki na wasu lokuta anan Nasarawa inda na kai matsayin akanta.

Daganan sai na shiga harkar siyasa inda na tsaya takaran kansila a inuwar Jam’iyyar UNCP inda aka bani lakabin ‘fatari mai ba wando kashi’. Ban samu nasara a zaben ba sakamakon magudi da akayi mani a lokacin. Daganan na samu mukamin shugabar matan jam’iyyar UNCP.

Na kuma kasance mace ta farko da ta rike mukamin shugabar matan jam’iyyar PDP a jihar nan, inda bayan na kammala wa’adina aka sake zabe ni a mukamin karo na biyu a shekarar 2000 kenan. Na kuma kasance mace ta farko da tsohon gwamnan jihar nan na farko a mulkin farar hula, sanata Abdullahi Adamu ya nada a matsayin Kwamishinan Hukumar Zabe ta jihar nan a lokacinsa.

Daganan na shugabanci cibiyar yaki da jahilci a jihar nan. Na kuma shugabanci wata qungiya mai zaman kanta da ake kira ‘project 50’ wanda ke tabbatar an samu gwamna da bai wuce shekaru 50 ba a jihar nan da kasa bakidaya. Da tsohon gwamnan jihar nan maigirma Umaru Tanko Almakura ya fito takara karo na fari a shekarar 2011 ne sai ya kuma nada ni a matsayin daraktan wayar da kawunan jama,a na kanfen dinsa.

Da ya sake samun nasara karo na biyu sai ya nada ni mai ba shi shawara ta musamman akan harkokin jam’iyyun siyasa a jihar nan wato daga shekarar 2012 zuwa 2013 kenan. Na kuma kasance Amiral hajj zuwa Kasar Saudiya har sau biyu a shekarar 2012 zuwa 2013. Na kuma riqe mukamin babbar mai bai wa gwamna Abdullahi Sule na jihar nan shawara ta musamman akan dukka harkoki da suka shafi nakasassun jihar nan bakidaya da kuma jinsi kafin yanzu da aka zabe ni mamba a majolisar dokokin Jihar Nasarawa, don wakiltal mazabar Nasarawa ta Tsakiya. Ka ji kadan daga cikin tarihin rayuwata.

Wadannan nasarori da ki ka samu ya sa ni kaiwa ga tambayar ko kin samu wasu sarautu na gargajiya da ki ke rike da su?

Tabbas na samu sarautu na gargajiya da suka hada da, Garkuwar Matan Nasarawa da Tauraruwan Matan Loko da Jarumar Matan Jihar da Tafisu na Matan Jihar Nasarawa da sauransu.

Za mu so jin wasu lambobin yabo da ki ka samu.

Daga cikinsu akwai Jarumar Matan Afirka Masu Gina Kasa da Ambsadan Zaman Lafiya na Kungiyar Universal Peace Federation na shekarar 2008 da Mamar Afirka wanda kungiyar Election Communication Limited ke bayarwa ta bani kwanakin baya da sauransu.

Sanar da mu kasashen da ki ka samu damar ziyarta.

To ni dai kawo yanzu da yardar Allah na ziyarci kasashe da dama inda na tafi wasu ayyuka da suka hada da Dubai da Indiya da Germany da Saudiya, inda na kai ziyara a Makka da Madina da dai sauransu. Kuma har yanzu nakan tafi kasashen a duk lokaci da na samu hutu ko idan wani aiki ya kai ni.

Sanar da mu irin tufafin da ki ka fi sha’awar sawa.

To ni dai na fi sha’awar in ganni cikin tufafi irin namu na matan Arewa kamar dai yadda al’adunmu ta tanada. Ka san anan gida Arewa an fi so a ga mace ta fita cikin mutunci da al’ada ba fita irin ta matan zamani ba. Kuma kamar yadda ka sani ni cikakkiyar ‘yar sarauta ce. Saboda haka ya zame min wajibi in rika fita irin ta gargajiya da kuma mutunci don ‘yan’uwana mata da ke tasowa su yi koyi da haka. Saboda haka a takaice kamar yadda na bayyana na fi so in gan ni akoyaushe cikin tufafi irin namu na matan Arewa da kuma gargaji. Ka ji wannan kenan.

Za mu so jin irin nasarorin da ki ka cimma a rayuwarki kawo yanzu.

A gaskiya ba wai yabon kai ko wani abu makamancin sa ba a yau zan iya cewa da yardar Allah na samu nasarori da dama a rayuwata. Ka ga kamar yadda na bayyana maka takaitaccen tarihina za ka iya lura cewa duk da Ina mace na rike ko ince na shugabanci kungiyoyi daban-daban da dama ciki har da na siyasa da sauransu. Haka kuma na samu farin jini agun galibin shugabannin jihar nan musamman tsofaffin gwamnoni da suka shude inda suka bani dama daban-daban na ba da tawa gudunmawa a matsayi daban-daban. Duk da Ina mace sun ga cancanta ta inda suka bukaci gudunmawa ta a bangaren shugabancin jihar nan.

Kuma kamar yadda ka sani na kawo cigaba da dama musamman a rayuwan ‘yan’uwana mata da nakasassu da sauran jama’a kawo yanzu ta hanyar kirkiro tare da aiwatar da ingantattun shirye-shirye da ke kawo canje-canje masu ma’ana a rayuwansu a kulla-yaumin. Kuma Ina ci gaba da yin haka har yanzu ban fasa ba.

Saboda haka a taqaice zance gaskiya na samu dinbin nasarori a rayuwata don Ina daya daga cikin fitattun matan jihar nan wadanda suke taka rawar gani a yau. Kuma kamar yadda na bayyana maka ba yabon kai ne ko wani abu daban ba, kai kanka kasan abin da nake nufi.

Wacce shawara ki ke da ita ga mata ‘yan’uwannki?

Shawara ta gare su akoyaushe ita ce, su tashi su nemi ilimin addini dana zamani don su ne ginshikin zaman duniya. Idan ba su da halin yin haka, sai su rungumi sana’a. kada mace ta dogara ga mijinta kawai a wannan zamani don idan ta yi haka zata fuskanci wulankaci. Haka kuma dole ‘yan’uwana mata su tabbatar suna bai wa ‘ya’yansu kwakkyawar kulawa ta wajen samar musu da ilimi mai inganci don ya taimaka wa rayuwansu a gobe.

Da me ki ke fatan a dinga tunawa da ke?

A gaskiya ni kam zan so a tuna da ni a matsayin mace da ta yi dukka mai yiwa wajen tallafa wa mata musamman wadanda suka rasa mazajensu da nakasassu da kuma marasa galihu a cikin al’umma. Don na lura da dadewa cewa wadannan mutane suna matukar bukatar taimakon kowa cikin al’umma.

Shi ya sa Ina so inyi amfani da wannan damar in yi kira na musamman ga masu hannu da shuni a qasar nan bakidaya da dukka gwamnatocin da ke kasar nan dukka mu hadu mu hada kai wurin ganin mun tallafi rayuwar marasa gata. Don AlIah a rika taimaka wa marasa galihu cikin al’umma akoyaushe. Kada mu manta cewa lalura ce ta samesu ba yinsu ba ne. Kuma idan mun taimaka musu ba shakka za mu samu lada daga Ubangiji tun anan duniya da kuma gobe kiyama.

Mun gode.

Ni ma na gode sosai.