Babbar mota ta markaɗe wata mata a yankin Abuja

Daga BASHIR ISAH

Wata tipa makare da yashi ta markade wata mata a cikin motarta a hanyar zuwa filin jirgin sama a yankin Lugbe, Abuja.

Binciken MANHAJA ya gano wannan mummunan al’amari ya faru ne a ranar Litinin da ta gabata biyo bayan akasin burki da motar ta fuskanta.

Hatarin ya haifar da tsaiko na wani lokaci a hanyar wanda hakan ya haifar da samun jerin gwanon motoci masu zaman jira a bude hanya.

Wani faifan bidiyon hatsarin da aka yada ya nuna yadda yashin da tipar ta dauko ya zuba a kan karamar motar da aka markade wanda jama’a suka yi kokarin bare motar kafin aka zagulo matar.

Bayanai sun ce, direban tipar ya tsallake rijiya da baya a hatsarin, amma ya tsere.

Hatsarin ya auku ne da misalin karfe 3 na rana a kusa da Aso Estate Junction, Lugbe, lamarin da ya haifar da cunkoson abubuwan hawa a yankin.

Daga bisani, an ga jami’an kiyaye hadurra, ‘yansanda da sauransu suna ta kokarin daidaita hanyar domin samun saukin zirga-zirgar abubuwan hawa.

Ya zuwa lokacin hada wannan labari, Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) ba ta ce komai kan batun ba.