Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ƙoli ta keɓe yanke hukunci kan zaɓen gwamnan Sakkwato

Kotun Koli da ke Abuja, ta kebe yanke hukunci kan karar da jam’iyyar PDP da dan takararta, Saidu Umar, suka daukaka na kalubalantar nasarar da Gwamna Ahmad Aliyu ya samu a matsayin zababben gwamnan jihar a zaben 2023.

Kwamitin akalai biyar karkashin jagorancin Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun, ya dauki wannan mataki ne yayin zaman shsari’ar da ya yi a ranar Laraba.

Kotun ta dage yanke hukunci kan shari’ar ne zuwa wani lokaci wanda ba ta ayyana ba. Kuma ta yi hakan ne bayan da ta karbi bayanai daga lauyoyin bangarorin da shari’ar ta shafa.