Da Ɗumi-Ɗumi: Ministan Lantarki, Adelabu ya yi murabus

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ministan Wutar Lantarkin Nijeriya, Adebayo Adelabu ya yi murabus daga muƙaminsa a hukumance domin mayar da hankali akan neman takarar gwamnan jiharsa ta Oyo.

A yau Talata Adelabu ya miƙa takardar yin murabus ɗinsa zuwa ga Shugaba Bola Tinubu ta hannun sakataren gwamnati.

Acikin wasiƙar, ya yi godiya ga Shugaba Tinubu bisa damar da ya ba shi ta yi wa ƙasa hidima, yana mai cewa ya ji daɗin gudunmawar da ya bayar wajen inganta ɓangaren wutar lantarkin Nijeriya.

A cewarsa, a yanzu hankalinsa zai karkata ne i’zuwa tsaya wa takarar gwamna a Oyo yayin da ake cigaba da tunkarar babban zaɓen 2027.

Gabanin ba shi muƙamin minista a gwamnatin Tinubu, Adelabu ya riƙe matsayin mataimakin gwamnan Babban Bankin Nijeriya, CBN.

By Babaji