
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A yau Talata ne aka sake mayar da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai hannun Hukumar Yaƙi da Rashawa (ICPC) domin ta cigaba da tsare shi bayan sakin sa na wasu kwanaki da aka yi a makon da ya gabata kan rasuwar mahaifiyarsa.
Rahotanni sun bayyana yadda aka sake gurfanar da shi a gaban kotu a yau, inda ya fara bayyana a Babbar Kotun Tarayya ta Jihar Kaduna akan wani sabon zargi da ICPC ta shigar a kansa.
Saidai rashin halartar wanda ake ƙara tare da shi ya sa aka ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 10 ga watan Afrilu, 2026.
Daga nan ne aka wuce da shi zuwa Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna domin sauraron buƙatarsa ta bayar da belinsa.
Da fari, kotun ta ɗage yanke hukunci akan buƙatar belin nasa zuwa ranar 31 ga Maris, 2026, wanda a zaman kotun na yau Talata, aka ji ta yi gum akan buƙatar belin, lamarin da ya ba wa ICPC damar sake kama shi zuwa lokacin da za a bada belin nasa.
