
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An samu sabon sauyi a tafiyar da harkokin siyasar Kano yayin da tsohon ɗan takarar gwamnan Jihar na jam’iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna ya koma jam’iyyar adawa ta ADC a cigaba da shirye-shiryen zaɓen 2027.
Rahotanni sun bayyana cewa, Gawuna ya yi rajista tare da karɓar katinsa na zama mamba a Gundumarsa ta Gawuna da ke Ƙaramar Hukumar Nassarawa a wani yanayi da dubunnan magoya baya da masu ruwa da tsaki suka shaida.
Nasiru Gawuna shi ne tsohon mataimakin gwamnan jihar har na tsawon shekaru huɗu da watanni takwas, wato daga Satumbar 2018 zuwa Mayu, 2023.
Daga cikin jiga-jigan siyasar jihar da suka halarci taron akwai jagoran Kwankwasiyya kuma tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, tsohon mataimakin gwamnan jihar, Aminu Gwarzo da kuma shugaban ADC na jihar, Musa Ungogo.
Da yake jawabi a taron, Gawuna ya bayyana godiyarsa ga magoya baya da jagororin jam’iyyar, yana mai alƙawarin yin aiki tuƙuru tare da su wajen ganin an ƙarfafa ADC a Jihar Kano.
