Daga UMAR GARBA a Katsina
Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina ta buƙaci wani Alhaji Jibrin Tanimu da ya janye zargin da ta bayyana a matsayin na ƙarya da kuma ɓata suna ga hukumar cikin kwana bakwai.
A cikin wata wasiƙa mai kwanan wata 29 ga Maris, 2026, wacce aka aika wa Tanimu a Modoji, ƙaramar hukumar Katsina, hukumar ta zarge shi da yin ikirarin cewa jami’anta sun sace masa Naira miliyan 221.
A cewar wasiƙar, an yi zargin ne a ranar ko kuma kusan 10 ga Maris, 2026, bayan da hukumar ta kama shi a gidansa.
Hukumar ta kuma yi zargin cewa Tanimu ba wai kawai ya yi iƙirarin a bainar jama’a ba, har ma ya sanar da su ta hanyar lauyoyinsa ga gwamnatin Jihar Katsina.
Ta bayyana zargin a matsayin “ƙarya tsagoronta, mugunta, kuma ba tare da wani tushe na gaskiya ba,” Hukumar Hisbah ta ce ɗan kasuwar yayi zargin ne don ɓata mata suna da kuma yaudarar jama’a da hukumomin gwamnati.
Wasiƙar, wacce Jabir Bello, babban lauya na Jiha kuma mai ba da shawara kan shari’a ga hukumar, ta bayyana cewa ayyukan Tanimu sun yi kama da ɓata suna, wanda ya haifar da mummunan tasiri ga hukumar, jami’anta, da ayyukanta.
Hukumar ta bayar da nata labarin abubuwan da suka faru, hukumar ta yi iƙirarin cewa ana binciken Tanimu ne bisa zargin karɓar Naira miliyan 10.2 ba bisa ƙa’ida ba daga mutane uku, Aminu Ado Yukasai, Mas’udu Armaya’u Abbas, da Aminu Garba Yakubu, dukkansu mazauna Jihar Kano.
Ta ƙara da cewa an gabatar da waɗanda abin ya shafa ga Tanimu ta hanyar wani jami’in Hisbah.
Hukumar ta kuma bayyana cewa wata kotu a Kano ta tsare waɗannan mutane, wadda daga baya ta ba da umarnin a gabatar da Tanimu a gaban kotu a matsayin sharaɗin sakin jami’in.
A matsayin wani ɓangare na buƙatunta, hukumar Hisbah ta umurci Tanimu da ya janye kalaman ɓatanci da ake zarginsa da aikatawa a rubuce nan take tare da bayar da haƙuri ga jama’a don a buga su a aƙalla jaridu biyu,
ta kuma umarce shi da ya daina yaɗa irin waɗannan iƙirarin da kuma tabbatar da yin abubuwan da aka buƙace shi cikin kwanaki bakwai bayan karɓar wasiƙar.
Hukumar ta yi gargaɗin cewa rashin yin waɗannan abubuwa da aka buƙace shi, hukumar ba ta da wani zaɓi illa ta ɗauki matakin shari’a, gami da neman diyya daga gare shi.
Hukumar ta kuma aika kwafin wasikar zuwa ga kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Katsina; daraktan hukumar tsaro ta Jiha, rundunar Katsina; Gwamnan Jihar Katsina da babban lauyan jiha.
