Soyayya kafin aure: Gari ya waye, amma hankali na barci

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

‘Soyayya kafin aure, tamkar cin abinci ne a kasuwa, ba a san lafiya ko cutar sa ba’

Mai karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin Iyali na jaridar Blueprint Manhaja. A wannan makon shafin zai yi dubiya ne kan yadda soyayyar yara kafin aure ke wanzuwa, me ke janyo ta, wane irin lahani take haifarwa, da kuma yadda za a magance ta cikin hikima.

Kafin komai zan faro da kai hanakalin mai karatu ga hanyar da rubutun nawa ya karkata. Soyayyar da take rubuce a wasu littafai musamman na Turawa a matsayin wayewa, soyayyar da ke ƙawata wa yaranmu fina-finan da suke kallo, wadda ake ganin idan ma ba ka yi, tamkar ba ka soyayya. Wannan ita ce soyayyar da ke lalata yara ‘yan makaranta, ke zubar da daraja, kuma ke rusa ginshiƙin al’umma tun daga tushe. Soyayya kafin aure ta zama wani tsari mai hatsari a cikin yara da matasa a yau, musamman ma a wannan zamani da wayar hannu da intanet suka zama wata mabuɗar ilimi mai kyau da kishiyarsa.

Mun kai lokacin da ba abinda za mu ce face Allah ya kawo mana ɗauki, domin ƙarshen zamanin nan da malamai ke sanar da mu alamomin zuwan sa, tabbas da yawa daga ciki sun bayyana, daga ciki akwai yawaitar zina, wadda da yawa take fakewa a rumfar soyayya. 

Abinda zai ƙara tayar da hankali kuwa, za ka samu yawaitar irin wannan soyayya ne a tsakanin matasa da a shekarun baya ko kusa ba su kai shekarun sanin hakan ba.

Wani malami daga Funtuwa ya bayyana cewa:

“Na kama ɗalibai biyu suna aika saƙonni masu zafi da hotuna a WhatsApp. Sun fara da ‘ina missing ɗinki,’ sun ƙare da ‘ka bani lokaci gobe da daddare.’”

Kamar wasa, soyayya da ya kamata a ajiyeta har bayan aure, yanzu tana afkawa yara ‘yan firamare da sakandare, tana haifar da barazana ga ilimi, tarbiyya da addini.

Me ke janyo soyayya kafin lokaci?

Rashin kulawa daga iyaye.

Kallon fina-finai da ke ɗauke da soyayya mai ɓata tarbiyya.

Amfani da wayoyi da intanet ba tare da kulawa ba.

Shagala da abokai masu ɗabi’a mara kyau.

Rashin ilmantarwa kan martabar jiki da iyaye suka gaza yi.

Illolin soyayya kafin aure:

Zubar da mutunci da daraja.

Yiwuwar samun ciki da auren dole ko zubar da ciki (abortion).

Rabuwar banza a makaranta da daina karatu.

Samun cututtuka kamar na jima’i (STDs).

Faɗuwar darajar iyaye da rushewar amana.

Rashin girmama aure da jin cewa soyayya ta isar ma.

A wata cibiya a Bauchi, an bayar da rahoton yara mata da aka kawo da ciki fiye da 23 a cikin shekara guda, dukkansu matasa ‘yan makaranta.

Yadda iyaye za su ba wa ‘ya’yansu kariya daga wannan matsala:

1. Rungumar yaro da soyayyar halal: Kada iyaye su bar yara su nemi kulawa daga waje.

2. Tattauna batun jima’i cikin hikima: Kada a ɓoye gaskiya ga yara masu tasowa.

3. Kula da wayoyi da intanet: A saka “parental control,” a sa idanu a dukkan abin da yara ke kallo.

 4. Kiyaye yara daga abokai masu ɓarna: Aboki na iya maye gurbin uba ko uwa idan an kyale.

5. Karantar da yara ma’anar soyayya ta Musulunci: Soyayya ba neman jiki ba ce, amana ce, shaƙuwa daga nesa ce, da mutunta haƙƙoƙin Allah.

Misalai daga gidauniyoyi da malamai:

A Kano, wata makaranta ta hana ɗalibai ɗaukar waya gaba ɗaya, kuma ta kafa ƙungiyar “Zaman Mutunci” don karantar da masu tasowa game da haɗurran wofantar da kai da darajar jiki.

A Birnin Kebbi, wata ƙungiyar malamai mata suna koyar da yara mata labaran sahabai da Annabawa, don su gane bambancin soyayya ta gaskiya da ta fim.

A Kaduna, wani malami ya ƙirƙiro “karatun hutun Lahadi” wanda ke jan yara daga titin soyayyar banza zuwa ilmantar da su da nishaɗi.

Daga ƙarshe muna kira ga iyaye da su kawar da son zuciya da ruɗin zamani na cewa wayewa ce barin yara suna irin wannan kusanci da ke kai su ga ɓarna. A koya wa yara soyayya da girmamawa, ba soyayyar da ke zubar da mutunci ba. A sanar da su cewar: lokaci yana da daraja, kuma jiki amana ne.

Yara su ne ginshiƙi, kuma su ne makomar al’umma. Idan aka bar su cikin harkar soyayyar banza, sai al’umma ta wayi gari ‘ya’yan sunna sun ƙaranta. Iyaye na da rawar da ba wanda zai maye musu, kuma addini na da tsari da shiriya.

By ukarofi