Da Ɗumi-Ɗumi: NAF ta fitar da sunayen mutane 25 da suka rasu a hatsarin jirgin sojoji a Ondo

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar Sojin Saman Nijeriya NAF, ta fitar da sunayen mutane 25 da suka rasu a hatsarin jirgin rundunar (ATR 42) da ya auku a yankin Igbokoda da ke Jihar Ondo a ranar Litinin. Rahotanni sun nuna cewa al’amarin ya faru ne a lokacin da jirgin na NAF 931 ke ɗauke da jami’an jirgi biyar da fasinjoji 20 yayin da yake kan hanyar zuwa Legas daga Benin.

A wata sanarwa da Kakakin NAF, Air Komodo Ehimen Ejodame ya fitar, ya ce babu wanda ya tsira daga iftila’in, wanda ya sanya hukumomin hanzarta gudanar da aikin bincike da ceto.

Waɗanda suka rasu sun haɗa da jami’an jirgi guda biyar: “Squadron Leader MI Aburime, the flight captain; Squadron Leader AP Man-Ugwueje, co-pilot; Flight Lieutenant IS Bako, co-pilot; Warrant Officer Abubakar A, aircraft technician; and Corporal Uguru HC, aircraft technician”, kamar yadda NewsPointNigeria ta wallafa.

Fasinjojin sune “Lieutenant TL Lazarus; Flight Lieutenant M Akinloye; Flying Officer IM Adeshina; Master Warrant Officer Onwuka F; Master Warrant Officer Matini BA; Warrant Officer Nuhu FS; Flight Sergeant James RB; Flight Sergeant Mohammed AI; Sergeant Ani AE; Sergeant Izibenikien SI; Sergeant Alafuka C; Sergeant Mbadugha AN; Lance Corporal Ugwuba FC; Lance Corporal Eledan GE; Mrs Ezeh Nneka; Godstmine Tarabina; Joy Micheal; Sunday Micheal; Ukeme David; and Gideon Omotola.”

Tuni dai Shugaban Rundunar Sojin Saman, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke ya bayyana jimaminsa da aika saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, abokan arziƙi da abokan aiki bisa rashin jami’an, yana mai bayyana hakan a matsayin babban rashi ga NAF da ma Nijeriya baki ɗaya. Ya tabbatar wa iyalansu samun cikakken tallafi a yayin jimamin.

Ya kuma bayar da umarnin a gudanar da cikakken bincike kan ainihin abin da ya sabbaba aukuwar lamarin. Sannan an buɗe ƙofar amsar gaisuwar ta’aziyya a Hedikwatar NAF da ke Abuja ga manyan jami’an gwamnati, mambobin jami’an difulomasiyya, jagororin hukumomin tsaro da sauran masu fatan alheri da masu jajenta wa iyalan da NAF akan abin alhinin.

Jami’an Gudanar da Jirgin sune: Squadron Leader MI Aburime — Flight Captain, Squadron Leader AP Man-Ugwueje — Co-Pilot, Flight Lieutenant IS Bako — Co-Pilot, Warrant Officer Abubakar A — Aircraft Technician da kuma Corporal Uguru HC — Aircraft Technician.

Fasinjojin sune kamar haka:

Flight Lieutenant TL Lazarus

  1. Flight Lieutenant M Akinloye
  2. Flying Officer IM Adeshina
  3. Master Warrant Officer Onwuka F
  4. Master Warrant Officer Matini BA
  5. Warrant Officer Nuhu FS
  6. Flight Sergeant James RB
  7. Flight Sergeant Mohammed AI
  8. Sergeant Ani AE
  9. Sergeant Izibenikien SI
  10. Sergeant Alafuka C
  11. Sergeant Mbadugha AN
  12. Lance Corporal Ugwuba FC
  13. Lance Corporal Eledan GE
  14. Mrs Ezeh Nneka
  15. Godstmine Tarabina
  16. Joy Micheal
  17. Sunday Micheal
  18. Ukeme David
  19. Gideon Omotola
wannan ɗaya ne daga cikin mamatan mai suna Man-Ugwueje da rahotanni suka ce an yi aurensa makonni biyu da suka gabaci aukuwar iftila’in
By Babaji

Leave a Reply