Yadda bashi ke rusa abota da zumunci tsakanin ’yan uwa da abokai

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Abota, zumunci da kyakkyawar alaƙa tsakanin abokai, abokan aiki da ’yan uwa na iya lalacewa sakamakon ba da bashi ko karɓar kuɗi aro, musamman idan wanda ya karɓi kuɗin ya gaza mayar da shi a lokacin da aka tsara.

A wannan rahoto, jaridar Blueprint Manahja ta duba dalilan da ke jawo irin waɗannan saɓani, rashin jituwa da rikice-rikicen da suka shafi kuɗi.

Akwai wata shahararriyar magana ta Lord Polonius ga ɗansa Laertes a wasan kwaikwayo na William Shakespeare mai suna Hamlet, wadda ke gargaɗin cewa mai ba da bashi ko mai karɓar bashi na iya rasa kuɗinsa da kuma abokinsa.

A rayuwar yau da kullum, abu ne da aka saba gani ko ji mutum yana roƙon abokinsa, abokin aikinsa ko ɗan uwansa ya ba shi kuɗi aro, tare da alƙawarin mayar da su a wani ƙayyadadden lokaci.

Sai dai idan lokacin da aka tsara ya yi, wasu daga cikin masu karɓar bashin kan fara guje wa kiran waya da saƙonnin wanda ya ba su kuɗin, ko kuma su ƙirƙiro wasu dalilai na neman jinkirta biyan bashin.

Wasu kan kawo uzuri na ban tausayi domin a ƙara musu lokaci, yayin da wasu kuma har sukan koma zagin wanda ya ba su kuɗin, lamarin da kan haifar da rashin jituwa da lalata alaƙar da ke tsakaninsu.

Abubuwan da mutane suka fuskanta:

Da take magana da Blueprint Weekend, wata ma’aikaciyar gwamnati a Abuja, Mrs Rita Etim, ta ce a halin yanzu tana fama da matsaloli tsakaninta da wasu ƙawayenta da ’yan uwanta saboda gaza mayar mata da kuɗin da ta ba su aro.

Ta ce ba ta fahimci dalilin da ya sa wasu mutane ke karɓar bashi ba tare da niyyar mayar da shi ba. A cewarta, masu neman bashi kan zo cikin ladabi, su ba da labaran matsaloli masu ban tausayi da za su sa mutum tausaya musu ya ba su kuɗi, amma da zarar sun samu abin da suke nema, sai su fara wahalar da wanda ya ba su kuɗin idan lokacin mayarwa ya yi.

Ta ba da misalin wata kawarta da ta roƙe ta kuɗi domin magance wasu matsalolin iyalinta. Ta ce duk da cewa ita ma ba ta da isasshen kuɗi a lokacin, ta ba ta Naira 100,000. Sai dai lokacin da aka zo batun mayar da kuɗin, ƙawar ta fara samun saɓani da ita. A cewarta, an yi ta samun husuma, zage-zage da kalaman ɓatanci kafin daga bisani ƙawar ta amince da biyan bashin a hankali.

Maimakon ta mayar da Naira 100,000 gaba ɗaya, ta fara biyan Naira 10,000 ko Naira 20,000 lokaci-lokaci har sai ta kammala bashin. Ta ce, daga nan ne alaƙarsu ta fara lalacewa, har suka daina magana da juna.

Etim ta kuma ba da wani misali na yadda ta ba wani ɗan uwanta Naira 350,000 domin ya taimaka masa wajen biyan kuɗaɗen jana’izar mahaifiyarsa, tare da yarjejeniyar cewa zai mayar da kuɗin cikin watanni shida Ta ce, kafin wannan, ita ma ta ba shi Naira 50,000 a matsayin tallafi na kyauta.

Sai dai daga baya ɗan uwan nata ya kasa mayar da dukkan kuɗin, inda ta samu damar karɓar Naira 150,000 kacal. A cewarta, lamarin ya jawo rikici har sai da ’yan uwa suka shiga tsakani suka roƙe ta ta haƙura da sauran kuɗin.

Bashin haya ya raba abokai:

Shi ma wani ɗan kasuwa a Jihar Legas, Peter Adebanjo, ya ce a yanzu ba ya magana da wani abokinsa tun yarintarsu saboda rashin mayar masa da kuɗin da ya ba shi aro domin ya cike gibin kuɗin hayarsa a shekarar 2022.

Ya ce wasu ’yan Nijeriya kan yi amfani da kyautatawar wasu, inda son kai, rashin godiya da rashin sanin ya kamata ke haddasa lalacewar alaƙa.

Ya ce ya fuskanci irin wannan matsala sau da dama daga wasu abokai da ’yan uwa da ya ba kuɗi aro, amma suka kasa mayar da shi, lamarin da ya tilasta masa ya haƙura da kuɗin saboda ya fara shafar sadarwa da alaƙar da ke tsakaninsu.

Adebanjo ya ce ya ba abokinsa Naira 200,000 domin ya cike kuɗin hayarsa, amma da lokacin mayar da bashin ya yi, abokin nasa ya fara guje wa kiransa tare da daina amsa saƙonninsa na waya da WhatsApp. Ya ce har lokacin da suka haɗu a wani taron jama’a, abokin nasa ya ce masa: “Ai Naira 200,000 ce kawai. Me ya sa kake damuna a kan Naira 200,000 kacal?”

Adebanjo ya ce abin mamaki shi ne, lokacin da abokin nasa ke buƙatar kuɗin, ba “Naira 200,000 kacal” ba ce, amma da lokacin mayar da su ya yi, sai ya mayar da kuɗin kamar ba su da wani muhimmanci. Ya ce abokin nasa har yanzu bai biya bashin ba, sai da wasu abokansu na bai ɗaya suka shiga tsakani kafin daga bisani ya amince zai mayar da kuɗin.

Saboda wannan ƙwarewa, Adebanjo ya ce ya yanke shawarar daina ba mutane kuɗi aro. Ya ce maimakon haka, idan mutum ya zo ya roƙe shi Naira 100,000, zai iya ba shi Naira 20,000 ko 30,000 gwargwadon abin da zai iya jure rashinsa. A cewarsa, ba zai gaya wa mutumin cewa kuɗin kyauta ne ba, domin idan bai mayar ba, ba zai dame shi ba.

Sai dai ya ce daga wannan lokaci, ba zai sake ba shi ko sisin kwabo ba ko da kuwa yana cikin matsananciyar buƙata, domin hakan ya zama sabuwar dokar da ya kafa wa kansa domin guje wa matsala da abokai.

Masana sun ba da shawara:

Wani akawunta a Abakaliki, Kingsley Chukwu, ya shawarci ’yan Nijeriya da su guji ba mutane kuɗi aro idan suna son kare alaƙarsu. Ya ce mutane da dama na da matsalar mayar da bashin da suka karɓa saboda dalilai daban-daban. Ya kawo wata magana daga harshen Igbo da ke nuni da cewa bakin da mutum ya yi amfani da shi wajen neman kuɗi aro ba shi ne bakin da zai yi amfani da shi wajen mayar da kuɗin ba.

A cewarsa, masu neman bashi kan je wurin ’yan uwa, abokai, makwabta ko abokan aiki cikin tawali’u da dabara, har su rantse da abubuwan da suke ganin masu tsarki ne domin su samu kuɗin tare da alkawarin mayar da shi a lokacin da aka tsara.

Sai dai da zarar sun samu bashin da suke tsananin buƙata, mayar da shi kan zama babban matsala. Ya ce mutum da a da yake yawan shiga cikin jama’a zai iya fara killace kansa saboda rashin iya biyan bashin da ya karɓa.

A cewarsa, mai bashi kan fara guje wa wanda ya ba shi kuɗin kai tsaye, har ma ya ƙi amsa kira ko saƙon waya. Chukwu ya ce duk da cewa yana da wahala, ya kamata mutane su rage ba da kuɗi aro.

A maimakon haka, ya ba da shawarar mutum ya ba wanda ke cikin buƙata duk adadin kuɗin da zai iya sadaukarwa ba tare da tsammanin za a mayar masa da su ba. Ya ce hakan ya fi ba da bashi wanda daga baya zai iya lalata alaƙar da ke tsakanin mutane.

Rashin biyan bashi na lalata mutunci:

Shi ma wani masanin tattalin arziki a Abuja, Sanusi Abdullahi, ya shawarci ’yan Nijeriya su kasance masu bin tsarin kula da kuɗinsu yadda ya kamata. Ya ce rashin mayar da bashi na iya yin mummunan tasiri ga mutuncin mutum.

A cewarsa, mutane da dama na samun wahalar mayar da kuɗin da suka karɓa saboda haɗuwar matsalolin tunani, halayen kashe kuɗi da kuma matsin tattalin arziki. Ya ce masu karɓar bashi kan fi mayar da hankali kan buƙatunsu na gaggawa fiye da abin da zai same su nan gaba idan lokacin biyan bashin ya zo.

Ya ƙara da cewa wasu mutane kan fara ɗaukar kuɗin aro kamar mallakarsu ne, don haka idan lokacin biyan bashin ya yi sai su fara guje wa mai bashin saboda kunya ko fargabar fuskantar sa. Abdullahi ya ce, a wasu lokuta matsalar tana farawa ne tun daga rashin bibiyar yadda ake kashe kuɗi a kowane mako, lamarin da ke sa mutum ya kasa ware abin da zai biya bashi. Ya ce ƙarancin kuɗin shiga, rasa aiki ko kuma tsadar rayuwa na iya cinye kuɗin da mutum zai yi amfani da shi wajen biyan bashinsa.

Haka kuma, wasu mutane kan kashe kuɗin aro wajen biyan buƙatun wucin gadi ko abubuwan more rayuwa maimakon saka su cikin abin da zai samar musu da kuɗin shiga. Ya ce wannan na faruwa ne saboda mutum ya karɓi bashin ba tare da ya tsara yadda zai samu kuɗin da zai mayar da shi ba.

Masanin ya kuma ce rashin rubutacciyar yarjejeniya, wa’adin biyan kuɗi ko hukuncin da za a fuskanta idan an karya yarjejeniyar na sa wasu mutane ɗaukar bashin da aka karɓa daga abokai ko ’yan uwa da wasa.

Ya ce, ba kamar bashin banki ko na wasu kamfanonin bayar da bashi ba, bashin da ake bai wa juna tsakanin abokai da ’yan uwa yawanci ba ya zuwa da ƙa’idoji masu tsauri ko sakamakon doka, abin da kan sa mai karɓar bashin ɗauka kamar kyauta aka ba shi.

Chukwu ya ƙara da cewa, masu karɓar bashi kan yi tunanin cewa ’yan uwa da abokai za su fi sassauci fiye da banki ko kamfanonin bayar da bashi idan sun kasa biyan bashin a kan lokaci.

Sai dai ya ce ƙin mayar da kuɗin da aka karɓa na iya haifar da babbar husuma da kuma karya amana tsakanin abokai da ’yan uwa. Ya ce alaƙar mutane tana dogara ne kan gaskiya da mutunta juna, don haka rashin mayar da kuɗi na iya sa wanda ya bayar da bashin ji cewa an ci amanarsa.

A gefe guda kuma, ya ce masu ba da bashi su ma kan ji kunyar neman a mayar musu da kuɗinsu, lamarin da ke ƙara haifar da tashin hankali da damuwa ga ɓangarorin biyu.

By ukarofi

Leave a Reply