Da Ɗumi-Ɗumi: Tinubu ya ƙara wa sojoji albashi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da yi wa albashin jami’an sojoji ƙari.

Hakan na zuwa ne kwanaki kaɗan da Ministan Tsaro Janar Christopher Musa (mai ritaya) ya ce kwanan nan Shugaban zai yi ƙarin albashi ga dakarun soji.

A ƙarƙashin sabon tsarin albashin, wanda zai fara aiki a ranar 1 ga Satumba, jami’an da ke muƙami sama da kanal za su samu ƙarin kaso 30 daga ainihin abin da suke karɓa a wata yayin da daga kanal zuwa ƙasa kuma za su amfani da tagomashin ƙarin kaso 50.

Sai kuma masu muƙamin ‘Private’ zuwa ‘Sergeant’, waɗanda za su samu mafi girman ƙari na kaso 80.

Wannan mataki ya nuna cewa ƙudirin albashin sojoji zai ƙaru daga Naira biliyan 660 zuwa biliyan N924.

Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga, wanda ya sanar da amincewar a ranar Talata, ya ce wannan mataki wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatin Shugaba Tinubu na inganta walwalar jami’an sojoji da kuma yaba wa sadaukarwa da ƙoƙarinsu wajen bai wa ƙasa kariya.

Kazalika, shugaban ya jinina wa dakarun bisa nuna jarumta da sadaukarwa wajen tunkarar ayyukan ‘yan bindiga, garkuwa, ta’addanci da sauran ababen da ke zama barazana a sassan ƙasar.

A cewarsa, gwamnatin nasa za ta cigaba da ƙoƙarin kula da walwalar sojoji yayin ƙara ƙarfafa su ta hanyar samar musu da makamai na zamani da bunƙasa harkokin fasaha a ayyukansu.

By Babaji

Leave a Reply