Sojoji sun kama mutum huɗu bisa zargin kai wa Boko Haram da ISWAP magani da wasu ababe a Borno da Yobe

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Dakarun tsaro na Atisayen Haɗin Kai da ke aiki a shiyyar Arewa maso Gabas, sun yi nasarar kama wasu mutane huɗu da ake zargi da aiki tare da mayaƙan Boko Haram da ISWAP wajen kai musu wasu kayayyakin amfanin yau da kullum.

Sojojin sun kuma kama wasu mutane 20 da ake zargin iyalan mayaƙan Jama’atu Ahlis Sunna Lidda’awati wal-Jiha ne da suka tsere daga sansaninsu a Ƙaramar Hukumar Konduga ta Jihar Borno.

Kyaftin Mohammed Goni, jami’in yaɗa labaran dakarun na riƙo ne ya bayyana haka a wata takarda da ya fitar a yau Talata.

Ya ce, an gudanar da atisayen ne bisa samun wasu bayanai na sirri da ƙoƙarin lalata hanyoyin da ‘yan ta’adda ke amfani da su wajen samun kayayyaki a shiyyar.

A cewar sanarwar, dakarun Bataliya ta 159 ƙarƙashin Sashe na 2 sun gudanar da atisayen ‘cordon-and-search’ a garin Geidam na Jihar Yobe a ranar 3 ga Agusta bayan samun wasu bayanan sirri. A yayin haka ne aka kama wasu mutum biyu bisa zargin samar wa ‘yan ta’adda magani da wasu kayayyaki.

Daga cikin ababen da aka ƙwato daga gare su akwai wani babban adadi na tabar wiwi, wayoyin hannu, injin caji, almakasai, wuƙaƙe, fitilu da maƙesta.

Haka kuma, sun ƙwato kwalin sigari, ƙwayar Pregabalin, Piscof syrup, katinan shaidar ƙasa da na banki da kuma tsabar kuɗi N14,530.

A wani atisayen a ranar, dakarun Sashen Garrison na 3 da ‘yan Bataliyar Reconnaissance, sun kama mutum biyu masu yi wa ISWAP safarar wasu kayayyaki a Ƙaramar Hukumar Monguno, Jihar Borno. An yi nasarar haka ne bayan wani binciken sirri a hanyoyin da ake zargin suna amfani da su wajen harƙalla da mayaƙan.

Daga cikin ababen da aka ƙwato a wajensu akwai kwali 11 na biskit da guda 192, kwalin madara, suga, sabulu, fitilun kai, gari da kuma maƙesta.

Kazalika, sun ƙwato wayoyin salula biyu, wata babbar wuƙa, guru, darduma, maganin gargajiya da kuma tsabar Naira N6,600.

By Babaji

Leave a Reply