IPAC ta yi jimamin ƙaruwar matsalar tsaro a Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Ƙungiyar gammayyar jam’iyyun siyasa a Najeriya, reshen Jihar Zamfara IPAC, ta bayyana babban damuwa kan taɓarɓarewar tsaro, halin da tattalin arziki da zamantakewa da al’ummar jihar suka tsinci kansu, da kuma yadda mulki ke tafiya a jihar, IPAC ta buƙaci Gwamna Dauda Lawal da Gwamnatin Tarayya su ɗauki mataki cikin gaggawa.

A wani taron manema labarai da aka gudanar a sakatariyar ta da ke Gusau a yau Talata, Shugaban IPAC na jihar, Hon. Sulaiman Salisu, ya ce sun fitar da wannan matsaya ne bayan taron gaggawa da suka yi tare da shawarwari da shugabannin jam’iyyu, mambobi, shugabannin al’umma, da sauran masu ruwa da tsaki daga ƙananan hukumomi 14 na Zamfara.

“IPAC, wadda ita ce ƙungiyar haɗin kan dukkan jam’iyyun siyasa masu rijista a jihar, ta lissafa muhimman abubuwa shida da ta gano bayan nazarin halin da ake ciki yanzu”.

Majalisar ta ce ayyukan ‘yan bindiga, satar mutane, da kai hare-hare kan al’ummomi na ci gaba da haifar da mawuyacin hali a tsakanin al’ummar jihar. Wannan ya haifar da asarar rayuka, gudun hijirar iyalai, a wasu ƙananan hukumomi.

Duk da cewa muna cikin lokacin noma, IPAC ta lura da cewa manoma da dama ba su samu taki, ingantattun iri, ko wasu kayan noma masu muhimmanci daga gwamnatin jihar ba.

Ƙungiyar ta gargaɗi cewa wannan na iya haddasa matsala ga samar da abinci a jihar da ta dogara da noma.

Ƙungiyar ta kuma nuna damuwa kan rahotannin cewa kuɗin da gwamnatin jihar take kashewa wajen gina hanyoyi sun yi yawa. Ta buƙaci gwamnatin jihar ta kasance mai gaskiya, lissafi, da tabbatar da an yi amfani da kuɗaɗen jama’a yadda ya kamata.

IPAC ta soki yadda ake mayar da hankali wajen gina ababen more rayuwa a cikin birnin Gusau kawai, yayin da al’ummomin karkara da yawa gwamnatin ta yi watsi dasu, tana mai cewa hakan ya haifar da rashin jin daɗi a tsakanin al’ummar yankin karkara”.

IPAC ta ce duk da kuɗaɗen da jihar ke samu daga asusun tarayya da kuma tallafin abokan hulɗa na ci gaba, mazauna jihar na ci gaba da fuskantar tsananin rayuwa, rashin aikin yi, da nau’ukan haraji da dama.

IPAC ta kuma nuna damuwa kan ƙarancin ba ‘ya’yan Zamfara ƙwararru damar riƙe manyan muƙamai da shiga cikin ayyukan ci gaba, duk da cewa akwai ƙwararrun ‘ya’yan jihar da za su iya riƙe muƙamai.

Ta yi nuni musamman ga wakilcin tarayya, inda ta ce ba a ba Zamfara isasshen kulawa ba dangane da tsaro da ci gaba.

IPAC ta bayyana cewa duk yananyin da Jihar Zamfara take ciki tana da Sanatan da ya zamo cikin Sanatoci mafiya tasiri a Arewacin Najeriya, Sanata Abdul Aziz Yari Abubakar, amma bai taba nuna damuwar sa a majalisa ba.

Majalisar ta kuma ce kasancewar ƙaramin ministan tsaro Bello Mohammed Matawalle daga jihar ya fito bai kawo wani amfani ba ga halin da ake ciki a jihar ba.

Ta buƙaci ’yan majalisar dokokin tarayya masu wakiltar Zamfara su ƙara ƙarfafa ƙoƙari wajen kare muradun alummar jihar musamman tsaro, da walwalar mazaɓun su.

Majalisar ta yi kira ga Gwamna Dauda Lawal da ya ɗauki matakai na gaggawa domin ƙarfafa tsaro, bayar da tallafin noma a kan lokaci, tabbatar da an raba ayyukan ci gaba daidai a cikin ƙananan hukumomi 14, da kuma inganta walwalar ‘yan Jihar.

IPAC ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta ba Zamfara fifiko ta hanyar ƙarfafa ayyukan tsaro da hanzarta shirye-shiryen ci gaba.

“IPAC Zamfara ta himmatu wajen yin aiki tare da gwamnatoci a kowane mataki, kuma za ta ci gaba da faɗa don ganin an aiwatar da manufofi da ayyukan da za su kawo zaman lafiya, adalci, ci gaba mai ɗorewa, da jin daɗin al’ummar Jihar Zamfara,” in ji shugaban.

By ukarofi

Leave a Reply