Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina ya ƙaddamar da aikin gina tagwayen hanya mai tsawon kilomita uku a garin Mashi, ƙaramar hukumar Mashi.
Aikin da zai laƙume Naira biliyan 4.5, kamfanin Mothercat za ta gudanar da aikin ƙarkashin sa ido na ma’aikatar ayyuka da gidaje.
A jawabin sa Gwamna Raɗɗa ya bayyana kasuwar Mashi a mafi girma a faɗin Jihar da ya ce idan an kammala aikin tagwayen hanyar zai taimaka wajen safarar kayan masarufi ba ma a cikin Jihar ba har zuwa wasu jihohin kudu na ƙasar.
Haka kuma tagwayen hanyar za ta taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin yankin da rage cunkosa a hanyar cikin garin Mashi, Dikko ya bayyana haka.
A jawabin kwamishinan ayyuka da gidaje Injiniya Sani Magaji Ingawa ya bayyana garin Mashi a matsayin cibiyar kasuwanci, noma sifuri domin haka ya ce bayan kammala hanyar zai taimaka ma tattalin ƙaramar hukumar Mashi da Jihar Katsina baki ɗaya.
Shima ɗan majalisar dokoki na ƙasa mai wakiltar ƙananan hukumomin Mashi da Dutsi ya yaba wa gwamna Dikko Raɗɗa bisa yadda gwamnatin sa ke samar da ababen more rayuwa ta hanyar bunƙasa harkar Ilimi, lafiya,noma da tallafa wa ƙananan sana’oi a birni da karkara na jihar.
A na sa ran nan da watanni shida za a kammala aikin tagwayen hanyar kamar yadda a kai yarjejeniya tsakanin ma’aikatan ayyuka da kamfanin Mothercat.
