Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a
Kungiyar Izalatul bidi’a wa iƙamatul sunnah reshen Jihar Katsina ta naɗa Dr Bashir Ruwan Godiya a matsayin sabon darakta janaral.
Naɗin ya zo ne a matsayin wani muhimmin ci gaba a jagorancin ƙungiyar a faɗin jihar.
Dakta Bashir Usman Ruwan Godiya Malami ne a sashen nazarin aikin jarida na kwalejin kimiyya da fasaha ta Hassan Usman Katsina Polytechnic.
Ya kuma riƙe muƙamin mai ba gwamna shawara kan Ilimi mai zurfi a Jihar lokacin mulkin tsohon gwamna Rt Hon Aminu Bello Masari.
Tuni ƙungiyar ta ba sabon daraktan janaral takardar kama aiki.
