Ƙungiya kare Pantami ta ce zarge-zarge da ake masa ba su da hujja

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe

Wata ƙungiya mai suna Coalition of Northeast Movement for Gombe ta yi watsi da zarge-zargen da ake yi wa tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin dijital, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, kan zargin mallakar wasu kadarori a Abuja ta hanyar da ba ta dace ba.

Ƙungiyar ta bayyana cewa zarge-zargen ba su da hujjoji, kuma tana ganin an yi su ne da manufar ɓata sunan tsohon ministan.

A cikin wata sanarwa da kakakinta, Kwamared Tasiu Pantami, ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta ce tana mayar da martani ne kan rahotannin da ke cewa wata ƙungiya mai suna Concerned Gombe Citizens ta kai ƙorafi ga hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (ICPC), tana neman a binciki Pantami kan zargin mallakar wasu kadarori masu tsada a habban birnin tarayya.

Ƙungiyar ta ce duk da cewa tana goyon bayan a riƙa binciken duk wani zargin cin hanci da rashawa, hakan dole ne ya kasance bisa hujjoji masu ƙarfi, ba zato ko yaɗa jita-jita ba.

Ta ce har yanzu ba a gabatar da wata takardar mallaka, bayanan kuɗi ko wata hujja da ke danganta Pantami da kadarorin da ake magana a kansu ba.

A cewar ƙungiyar, Pantami ya yi aiki a gwamnatin tarayya ne bisa tanadin doka, kuma ya cika dukkan ƙa’idojin bayyana kadarori da ake buƙata daga jami’an gwamnati.

“Ba daidai ba ne a ɓata sunan mutum saboda zargi marar hujja. Idan akwai sahihan bayanai da ke nuna an aikata laifi, hukumomin da abin ya shafa su gudanar da bincike bisa doka. Amma bai kamata a riƙa yi wa mutane shari’a ta kafafen yaɗa labarai ba,” in ji sanarwar.

Ƙungiyar ta kuma yi kira ga hukumar ICPC da sauran hukumomin da abin ya shafa da su gudanar da aikinsu cikin adalci, ba tare da son rai ko nuna bambanci ba.

Har ila yau, ta gargadi ƙungiyoyi da masu fafutukar tabbatar da gaskiya da su guji gabatar da zarge-zargen da ba su da tushe, tana mai cewa hakan kan raunana yaƙi da cin hanci da rashawa.

A ƙarshe, ƙungiyar ta jaddada cewa tana goyon bayan yaƙi da cin hanci da rashawa, amma ta ce dole ne a gina wannan yaƙi a kan hujjoji, bin doka da tabbatar da adalci.

Ta ce, “Yaƙi da cin hanci bai kamata ya zama hanyar ɓata sunan mutane ba. Zargi kaɗai ba hujjar aikata laifi ba ce, kuma kowane ɗan ƙasa na da haƙƙin a yi masa adalci.”

By ukarofi

Leave a Reply