Da Ɗumi-Ɗumi: Tinubu ya sallami Bichi, ya naɗa sabbin shugabannin DSS da NIA

Spread the love

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa Adeola Oluwatosin Ajayi a mastayin sabon shugaban hukumar ‘yan sandan farin kaya (DSS)

Ajayi zai maye gurbin Yusuf Magaji Bichi wanda shine shugaban hukumar tun lokacin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Sannan ya naɗa Ambasada Muhammad Muhammad a matsayin shugaban hukumar leƙen asiri na Nijeriya bayan murabus ɗin tsohon shugaban Ahmed Rufai.

Wannan sanarwar ta fito daga bakin mai ba shugaban ƙasa shawara a fannin yaɗa labarai Ajuri Ngelale.

By ukarofi