‘Yan sandan da aka kashe: Kun farar da yaƙi a tsakaninmu – Kwamishinan ƴan sandan Abuja ga ƴan Shi’a

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Kwamishinan ƴan sandan Abuja, Benneth Igweh ya bayyana rashin jin daɗinsa game da kashe wasu jami’ansu guda biyu da aka yi a yayin wani zagaye na mambobin Shi’a.

Ya bayyana hakan a matsayin salo na fusatarwa wajen kai hari ga jami’an tsaro wanda hakan bai bar wasu mata guda biyu ba da aka raunata a yayin aukuwar lamarin a Abuja.

Rahotanni sun nuna cewa an harbe wani ɗan kasuwa har lahira tare da kashe ƴan sanda biyu a lokacin da aka yi artabu tsakanin ƴan sanda da ƴan Shi’a tare da ƙone motocin ƴan sanda uku a yankin kasuwar Wuse.

A lokacin da ya ke magana da ƴan jarida a hedkwatar rundunar, Kwamishinan ya ce ba zai lamunci kowane irin hari akan mutanensa ba, ya na mai tabbatar da cewa mutuwar ƴan sandan ba zata wuce haka kawai ba.

Ya ƙara da cewa, “ku ga yadda waɗannan mutanen suka kashe mun mutanena. Sannan suka raunata ƴan sanda mata biyu. In taƙaice mu ku, sun farar da yaƙi da jami’an tsaro.”

Kazalika, Kwamishina Igweh ya tabbatar da cewa wannan shine zagaye na ƙarshe da zasu yi a Abuja.

By Babaji