Kwanaki kaɗan da kisan Sarkin Gobir, ƴan bindiga sun yi garkuwa da mutum 150 a Gobir

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Aƙalla mutane 150 tare da dabbobi guda 1,000 ne ƴan bindiga suka yi garkuwa dasu a wasu ƙauyuka da ke yankin Masarautar Gobir a jihar Sakkwato.

Hakan ya faru ne a ƙasa da kwanaki uku da kisan Sarkin Gobir, Alhaji Isa Muhammad Bawa da ƴan bindiga suka yi bayan sun yi garkuwa da shi wanda kuma shi ne Hakimin Gatawa.

Bayan haka ne aka samu wani faifan bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta inda aka ga Sarkin an ɗaure masa ƙafafu da hannaye ya na magiya ga gwamnatin Sakkwato, Fadar Sarkin Musulmi, ƴan uwansa da abokai kan cewa su biya kuɗin fansar da ƴan bindigar suka buƙaci a ba su don ceto shi daga halin da ya tsinci kansa.

Hallau, ya ce ƴan bindigar sun iyakance lokacin karɓar kuɗin wanda rashin yin hakan, ka iya sanya su kashe shi.

Baya ga kashe Sarkin ne, sai ɗaruruwan matasan suka soma zanga-zanga a sakamakon haka wanda ta kai ga gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita a ƙaramar hukumar Sabon Birni inda Masarautar Sarkin take.

A lokacin da ya ke magana game garkuwa da aka yi da mutane a kwanan nan, Farfesa Bello Bada na jami’ar Usman Ɗanfodiyo ya ce abin takaici ne ace ƴan bindiga sun sake kai farmaki a yankin bayan kwanaki kaɗan da kisan Sarkin.

Bayan kwana ɗaya da kisan Sarkin ne ƴan bindiga suka sake kai farmaki ƙauyen Tsamaye inda suka kashe wasu mutane tare da yin garkuwa da wasu da ba a san adadinsu ba.

By Babaji