
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Ministan ma’aikatar Ilimi, Tahir Mamman ya ce ba za a sake barin ɗaliban da shekarunsu ya gaza ba su rubuta jarrabawar kammala sekandire.
Ministan ya faɗi haka ne a lokacin da ake hira da shi a tashar telebijin na ‘Channels’ inda ya ce gwamnatin tarayya ta umarci ofisoshin kula da jarrabawar ɗaliban sekandire na yammacin Afirka (WAEC) da ke bayar da shaidar WASSCE da kuma na jarrabawar Ƙasa (NECO) da ke shirya SSCE su tabbatar ɗalibi ya kai shekaru 18 kafin a bashi damar rubuta ɗaya daga cikin jarrabawar.
Sannan ya nanata cewa, game da jarrabawar kafin shiga jami’a ta UTME da hukumar haɗaka ta bada gurbin karatu ga ɗalibai a jami’o’i (JAMB) ke shiryawa, wajibi ne sai ɗalibi ya kai shekaru 18 kafin a bashi damar rubutawa.
Ya ce, dokar bai sabuwa ba ce, ta na cikin dokokin rubuta jarrabawar tsawon lokaci don haka ya ke kira ga al’umma su faɗaka.
Ya ƙara da cewa, don kaucewa shiga sahun waɗanda za a hana rubuta jarrabawar, akwai buƙatar iyaye su kiyaye wajen tabbatar da cewa ɗansu kar ya fara aji ɗaya a matakin firamare har sai ya kai shekaru shida.
Idan aka haɗa da zamansa a firamare da shekaru shida na sekandire hakan zai zama ya kai adadin shekarun da ake buƙata wajen bashi gurbin jarrabawar.
