LAFIYA UWAR JIKI: Olsa gyambon ciki (2)

Spread the love

Masu karatu barkanmu da wannan lokaci. Sannunmu da sake saduwa a wannan shafi na Lafiya360

A rubutun da ya wuce, na gabatar muku da olsa, me ce ce ita, yanayinta, bigirenta, da kuma yaɗuwarta a duniya. In sha Allah zan ɗora daga inda na tsaya. 

Yadda Olsa ke samuwa

Ciwon olsa na kama mutum ne a lokacin da aka samu rashin daidaito tsakanin abubuwan da ke kare tumbi /jakar da binci ke taruwa, daga ƙwayoyin cuta da kuma ruwan acid mai narka abinci DA kuma abubuwan da ke lalata wannan garkuwa ko kariya. A turance ana kiransu (Protectiɓe factors and Aggressiɓe Factors). 

Idan aka yi rashin dacewa abubuwan da ke lalata garkuwar tumbi su ka rinjayi abubuwan da ke samar da kariyar, to sai ciwon olsa ya kama ɗan adam. 

Ga misalan abubuwan da ke bawa jakar abinci kariya daga haɗari: 

A. Sinadarai 

(Sinadarin HCO3– , da Majina wato mucus da kuma Yalwataccen jini da ke kai komo.)

Shi baikabonet (HCO3) ya na taimakawa wajen kare tumbi daga illar acid na ciki wanda zai iya zaizaye shimfiɗar jakar abinci, daga nan sai a samu gyambon ciki. Aikinsa shi ne surka ruwan acid ɗin. 

Ita kuma majinar ta na kasancewa tamkar shimfiɗa da ke rufe bango da tsandaurin da ke farfajiyar tumbi, ta yadda ko da acid ya zuba a inda ba so, to ba zai taɓa jikin tumbin ba sai dai ya samu shimfiɗar majinar. 

Sai kuma isassen jini. Shi kuma aikinsa shi ne kawo abubuwan da ƙwayoyin halittar da ke wannan waje abubuwan da suke buƙata irin su isakar oksijin domin a gudanar da ayyuka yadda ya kamata. Ayyukan su ne: narka abinci, chakuɗa shi, tura abincin gaba izuwa hanji. 

B. Halittu

A halittun da ke bayar da wannan kariya akwai tantani, da kuma ƙwayoyin halittun da suka gina tumbi. 

Tantani ne na musamman da yake aiki irin na majinar da nayi bayani a baya.ya na kasancewa wata shifiɗa da ke bada kariyta kuma ana samiunsa a cikin tumbi da hanji. A turance ana kiransa da phospholipid layer. 

Su kuwa ƙwayoyin halittu da su ka gina tumbi aikinsu wanda ke tabbatar da samun kariya guda biyu ne: 1. Mommotsawa da yadda za su chakuɗa abinci da ruwan sinadaran da ke tumbi. Sannan na 2. Hayayyafa saboda a maye gurbin halittu da suka gaza ko su ka tsufa. Cikin hikimar Sarkin halitta, ana sauya ƙwayoyin halittun da abinci ke bi takansu wato Alimentary tract, tun daga baki har zuwa dubura a tsakanin kwanaki biyar zuwa bakwai. Saboda kullum sai munci abinci, wanda hakan zai iya sanya su saurin gajiya da saurin tsufa. 

Sababan Olsa:

Waɗannan su ne abubuwan da ke yaƙi da garkuwar da ke hana samuwar olsa. 

1. ruwan acid da cikin tumbi

2. ƙwayar cutar Helicobacter pylori (ta na kawo olsa)

3. Magungunan gajiya da ciwon gaɓoɓi (ibuprofen, ibumol, diclofenac)

4. Taba 

5. Giya

Haɗarin Kamuwa da Olsa:

1. Gado: idan mutum ya na da shaƙiƙi ko uwa ko uba masu olsa, shi ma nan gaba zai iya samun olsa, musamman idan akwai ƙwayar cutar Helicobacter pylori

2. ƙwayoyin cuta : herpes, TB, 

3. Magunguna irin su diclofenac, Potassium chloride, Steroids

4. Wahala: wahala ta na tayar da olsa ga wanda ya kasance tun asali ya na da ita. 

Ku ci gaba da bibiya ta domin kawo ƙarashen wannan rubutun. Insha Allah zan kawo yadda olsa ke kama mutum, alamominta, da illolinta, da wahalhalun da ta ke jefa mutum da kuma dabarun kiyaye tashinta. Ku tara

Idan kun amfana da wannan rubutu, ku yi sharing domin wasu su amfana. Na gode.

Naku, MI Abdullahi

Mustapha Ibrahim Abdullahi

By ukarofi