
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
A gobe Lahadi ne Mai Girma Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu zai gabatar da jawabi wa ƴan Nijeriya game da batun zanga-zangar tsadar rayuwa da ake yi a sassa daban-daban na faɗin ƙasar.
Mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale ya faɗi hakan cikin wata takarda da ya fitar a ranar Asabar, ya na mai cewa Tinubu zai yi jawabin ne a ranar 4 ga watan Agusta da misalin ƙarfe 7 na safe.
Ya yi kira ga gidajen jaridu kamar su telebijin da rediyo su kasance a shirye don ɗaukar jawabin kai-tsaye.
Sannan za a sake maimaita shi a gidajen telebijin na NTA da rediyo Nijeriya da misalin ƙarfe 3 na rana da kuma 7 na yamma.
