Zanga-zanga: An zargi na hannun daman Ganduje da iza wutar tashin-tashina a Kano

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Wata ƙungiyar kishin al’ummar jihar Kano mai suna ‘Civil Liberty Organization’, ta zargi ɗaya daga cikin na hannun daman Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa kuma tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, sannan sabon Darakta Janar na Cibiyar Bunƙasa Ƙasa, Baffa Babba Ɗan-Agundi, da ɗaukar nauyin wasu ɓata-gari da su ka haifar da tashin-tashina a jihar a ranar farko ta zanga-zangar tsadar rayuwa.

Jaridar ‘DAILY NIGERIAN’ ta ruwaito cewa, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanya dokar hana fita a jihar bayan da wasu ɓata-gari su ka shiga sace-sace da salwantar da dukiyar al’umma da ta ƙasa a lokacin zanga-zangar.

Haka nan, an ga Babba Ɗan-Agundi, wanda tsohon ɗan majalisar dokokin jihar ne ya jagoranci wasu masu zanga-zanga zuwa Fadar Nasarawa inda a nan ne saukakken Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ke zama.

Wani jawabi da Ghali Bala Ɗantata ya fitar, ya ce, ƙungiyar ta buƙaci a tuhumci Ɗan-Agundi, wanda aka ruwaito cewa an gan shi ya na shirya wasu mutane daban da masu zanga-zangar a cikin waɗansu bidiyoyi da su ka zagaye kafafen sadarwa.

Ƙungiyar ta bayyana cewa, “yayin da masu zanga-zangar su ka taru don bayyana kokensu kan gwamnatin, sai taron ya sauya zuwa hargitsi a lokacin da ake zargin Ɗan-Agundi ya isa wajen tare da wasu gungun ɓata-gari.”

Haka kuma, ƙungiyar ta caccaki kwamishinan ƴan sandan jihar saboda ƙyale Ɗan-Agundi da ya yi na jagorantar zugar da ba ta masu zanga-zanga ba ce.

Sai dai, a lokacin da aka tuntuɓe shi don jin ta bakinsa, Ɗan-Agundi bai bayar da gamsashshen bayani game da batun zargin ba, ya na mai cewa ba zai yi bayani kan zargin da bai san daga wani mutane bane ba.

By Babaji