Mu na so Tinubu ya taɓo batun haƙƙin waɗanda aka kashe a jawabinsa – AAC

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Yayin da aka samu sanarwar jawabin da Shugaba Tinubu zai yi a gobe Lahadi, jam’iyyar AAC ta ɓukaci gwamnatin tarayya ta bi haƙƙin waɗanda su ka rasa rayukansu a wajen zanga-zangar tsadar rayuwa a sassan Nijeriya.

Sakataren hulɗa da jama’a na Ƙasa a jam’iyyar, Femi Adeyeye ya faɗi hakan cikin wata takarda da ya fitar, inda ya ce sanarwar jawabin raina hankulan ƴan Nijeriya ne da su ka yi kwana uku su na fitowa zanga-zanga, ya na mai cewa ya kamata a gabatar da jawabin tun kafin wannan lokacin.

Ya ce sauya taken Ƙasa bai ɗauki sama da kwana biyu ba. Haka ma naɗa ministoci 48 da wasu mashawarta mara sa amfani.

Adeyeye ya ƙara da cewa, a matsayinsu na ƴan gaba-gaba wajen yin zanga-zangar, sun fahimci akwai danniya a matakai da dama aka ɗauka ciki har da kashe-kashe da cin mutuncin masu zanga-zangar da suka haɗa har da yara ƙanana da mata a jihohin Delta, Kano da ma Abuja wanda har yanzu ana cigaba da yi.

Mista Adeyeye ya ƙara da cewa, la’akari da faruwar wasu abubuwan, sun sha yin gargaɗin cewa gwamnatin ta fi mayar da hankali wajen sanya al’umma cikin halin ƙunci da zubda jini.

Dan haka, jam’iyyar ta buƙaci Shugaba Tinubu ya binciki dukkan masu-ruwa-da-tsaki game da aika-aikan da aka yi wa masu zanga-zangar tare da hukunta su, sannan ya bayyana matsayarsa game da hakan a yayin jawabinsa a gobe Lahadi.

By Babaji